1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda fiye da 70

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
April 17, 2022

A daidai lokacin da matsalolin tsaro ke kara ta'azzara a Najeriya, rundunar sojin kasar ta yi shelar kashe mayakan ISWAP fiye da 70 a yankin Tafkin Chadi mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/4A2ri
Symbolbild | Nigeria | SWAT
Hoto: Imago Images/ZUMA Press/Planetpix/A. F. E. Lii

Kakakin rundunar sojin saman Najeriya Edward Gabkwet, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar an kaddamar da luguden wuta kan mayakan ne bayan da aka tantance maboyarsu ciki har da wani sansanin atisayen da mayakan ke amfani da shi a kauyen Tumbun Rego da ke yankin Tafkin Chadi a ranar 14 ga wannan wata.

A baya-bayan nan dai runudunar tsaron ta Najeriya ta tsananta kai farmaki a kan mayakan masu da'awar jihadi a yankin Arewa maso gabashin kasar, tare da kara matsa kaimi ga 'yan fashin daji da masu garkuwa da jama'a da suka yi kaka gida a jihohin Arewa maso yammacin kasar, inda kuma ta ce tana samun nasara.