1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta tabbatar da daukan nauyin Wagner

Suleiman Babayo LMJ
June 27, 2023

Shugaban Rasha Vladimir Putin na Rasha ya ce gwamnatin kasar take tafiyar da sojojin haya na kamfanin Wagner wajen samar da kudin tafiyar da mayakan.

https://p.dw.com/p/4T87n
Rasha l Shugaba Vladimir Putin
Shugaba Vladimir Putin na RashaHoto: Sputnik/Sergei Guneev/Pool via REUTERS

Shugaba Vladimir Putin na Rasha a karon farko ya tabbatar da cewa gwamnati take biyan kudin tafiyar da sojojin haya na kamfanin Wagner wadanda suka yi bore a karshen mako.

Lokaci wata ganawa da dakarun kasar Putin ya ce gaba daya kudin tafiyar da kamfanin na wuyar gwamnatin kasar.

Haka na zuwa bayan yunkurin da mayakan suka yi na kutsawa zuwa birnin Moscow fadar gwamnatin kasar ta Rasha, domin nuna fushi kan yadda yakin da ke faruwa da Ukraine ke tafiya.

Yanzu haka Shugaba Alexander Lukashenko  na kasar Belarus ya tabbatar da cewa Yevgeny Prigozhina shugaban kamfanin sojojin hayan na Wagner yana kasarsa, kamar yadda aka tsara bisa hanyoyin kawo karshen boren da Rasha ta fuskanta.