1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTimor ta Gabas

An kama wadanda ake zargi da hare-hare a kasar Iran

January 6, 2024

Hukumomi a Iran sun tabbatar da kama wasu mutane da ake zargi da hannu cikin hare-haren nakiyoyi da suka yi sanadiyyar kashe kusan mutum 100 a ranar Larabar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/4av8x
Mutane na watsewa a wajen harin Kerman a Iran
Mutane na watsewa a wajen harin Kerman a IranHoto: MEHR NEWS/AFP

Hare-haren da kungiyar IS ta dauki alhakin kai su, sun rutsa ne da gomman mutanen a lokacin da ake tunawa da kisan jagoran mayakan juyin juya halin kasar Janar Qassem Soleimani, wanda Amurka ta halaka a ranar 3 ga watan Janairun 2020.

Mataimakin ministan cikin gida a Iran, Majid Mirahmadi ya ce ana tsare da wasu mutum biyar wadanda aka kama daga lardunan kasar dabam-dabam.

An kuma gudanar da jana'izar wadanda suka mutu a hare-haren a masallacin Amam Ali da ke Kerman, wanda ya samu halartar Shugaba Ebrahim Raisi.

Jagoran rundunar mayakan juyin juya halin kasar na yanzu, Hossein Salami ya karyata batun cewa kungiyar IS ce ta kai hare-haren tare da nuna cewa babu wani abin da ya saura na kungiyar, in banda wadanda Amurka da Isra'ila ke amfani da su a matsayin sojojin haya.