1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Harin bam ya kashe sama da mutum 100 a Iran

Zainab Mohammed Abubakar
January 3, 2024

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana alhininsa game daharin da hare-haren da suka hallaka sama da mutum 100 a Iran, a yayin da ake adduo'in tunawa da marigayi Janar Qasem Soleimani a mahaifarsa.

https://p.dw.com/p/4apoH
Hoto: MEHR/AFP

Cikin wata wasika da Putin ya aikewa shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi da kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Ali Khamenei ya ce "Kisan bayin Allah da suka ziyarci makabarta abin ban tsoro ne da rashin tausayi da kuma nuna kyama."

A yau da rana ne dai wasu tagwayen bama-bamai suka fashe a yayain da ake addu'oin tunawa da wani fitaccen Janar na Iran da aka kashe a wani harin da jiragen yakin Amurka maras matuki suka kai a shekarar 2020.

Jami'ai a Iran sun ce akalla mutane 103 ne suka mutu daura da wasu 211 da suka jikkata, wanda ke zuwa a daidai lokacin yankin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da fuskantar yakin da Isra'ila kaddamar kan Hamas a Zirin Gaza.

Ita ma dai Kungiyar Tarayyar Turai ta yi tir tare da yin kiran da a gurfanar da wadanda suka kai tagwayen hare-haren da suka yi sanadiyyar rayuka.