1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai harin bam a kasuwar birnin Diffa

February 8, 2015

Wannan harin ya zo ne a daidai lokacin da sojojin Nijar suke ci gaba da fatattakar 'yan Boko Haram a birnin na Diffa.

https://p.dw.com/p/1EXys
Nigeria Soldaten Boko Haram ARCHIVBILD
Hoto: Reuters

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa, 'yan kungiyar Boko Haram sun kai wani sabon hari da sanyin safiyar wannan Lahadin a birnin Diffa da ke gabashin kasar, tare da tayar da wani bam a kasuwar birnin na Diffa inda akalla mutun guda ya rasu, yayin da wasu akalla goma suka jikkata a cewar wata majiya ta jami'an agaji na wannan birni. Dakarun sojan Nijar dai sun fatattaki 'yan kungiyar ta Boko Haram da suka kai hari tare da harbe-harbe da manyan bindigogi a kewayen birnin mai makwabtaka da Tarayyar Najeriya. Mazauna a birnin sun ce suna yi ta jin karan harbe-harbe a wajan gari yayin da ake gwabza fada mai tsanani a kusa da wata gada da ke kusa da birnin.

Wannan dai shi ne karo na biyu da 'yan kungiyar ta Boko Haram suke kai hari cikin wannan jiha inda na farko ya wakana a ranar Jumma'a da ta gabata a garin Bosso da ke cikin jihar ta Diffa, wanda ya yi sanadiyar rasuwar jami'an tsaron Nijar guda hudu da farar hula guda, sannan aka kashe akalla mayakan Boko Haram 109.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita. Mohammad Nasiru Awal