1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An jefi motar shugaban ƙasar Najeriya a Yuganda

May 12, 2011

'Yan sandan Yuganda sun buɗe wuta kan matasa da suka riƙa jifar motar da ke ɗauke da shugaba Goodluck Jonathan a Kampala

https://p.dw.com/p/11F2a
Goodluck Jonathan Shugaban ƙasar' Najeriya da Mataimakinsa Namadi SamboHoto: AP

Masu aiko da rahotanin daga Yuganda sun ce 'yan sanda sun buɗe wuta akan wani gungun jama'a da suka riƙa jifa da duwatsu akan motar da ke ɗauke da shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan a sa'ilin da ya ke kan hanyar sa ta hallartar wurin bikin rantsar da shugaba Yoweri Museveni kuma har sun kashe mutun daya.

Ko da shi ke har ya zuwa yanzu ba a san dalillan da ya sa jama'ar yin jifar ba, amma 'yan sanda sun kame mutane da dama daga cikin waɗanda suka yi jiffar .An rantsar da sabon shugaban ƙasar Yuganda Yoweri Museveni tare da hallatar shugabannin ƙasashen Kwango da Zimbabuwe da Najeriya da Somaliya da kuma na yankin Kudancin Sudan a birnin kampala.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman