1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An fitar da ran samun mutane 20 da kasa ta binne Najeriya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 12, 2024

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger Ibrahim Audi Husseini, ya ce sun fitar da ran samun mahakan a raye ne bayan da suka shafe kwanaki 8 a karkashin kasa

https://p.dw.com/p/4gwL5
Hoto: Conceição Matende/DW

Hukumomi a Najeriya sun sanar da cewa sun fitar da ran samun ragowar masu numfashi a aikin ceto masu hakar ma'adanai su 20 da suka rage karkashin kasa, bayan da kasar ta binne su kusan kwanaki 10 da suka wuce a kauyen Galkogo na karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger.

Karin bayani:Gwamnati ta dakatar da hakar ma'adanai a Zamfara

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger Ibrahim Audi Husseini, ya ce sun fitar da ran samun mahakan a raye ne bayan da suka shafe kwanaki 8 a karkashin kasa, ko da yake basu kawo karshen aikin ba a hukumance.

Karin bayani:Ana cikin fargaba na neman masu hakar zinare a Najeriya

Ibrahim Audi Husseini ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa rashin isassun kayan aikin zakulo mutanen ne ya tilasta su amfani da hannu wajen aikin tonon tare da kawar da duwatsun da suka kewaye ramin da mutanen ke ciki.