1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Rasha: Shekara guda da mutuwar Navalny

February 16, 2025

Shekara guda bayan mutuwar babban dan adawar Rasha Alexei Navalny magoya bayansa, sun shirya bukukuwa a cikin da wajen kasar domin tunawa da gwagwarmayar da ya yi kafin rasuwarsa.

https://p.dw.com/p/4qYQg
Lettland Riga | Trauer nach Tod von Alexei Navalny
Hoto: GINTS IVUSKANS/AFP/Getty Images

Darurruwa mutane sun ziyarci kabarin marigayi Alexei Navalny a birnin Moscow albarkacin zagoyowar cika shekara guda da mutuwar babban dan adawar na Shugaba Vladmir Putin.

Duk da barazanar da suke fuskanta daga fadar mulki ta Kremlin da kuma tsananin sanin da ake yi, magoya bayan Navalny da ya mutu a gidan yari sun fita kwansu da kwarkwatarsa domin ajiye furanni a gaban kabarin marigayin a matsayin girmamawa. 

A hannu guda kuma mai dakinsa Madam Yulia Navalnaya da ke halatar wani taron gangami da aka shirya a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus ta bukaci magoya bayansa da su ci gaba da gwagwarmaya domin 'yantar da Rasha, kokawar da Navalny ya sadaukar da rayuwarsa a kanta.

Karin bayani: Jagoran adawar Rasha Alexei Navalny ya mutu a kurkuku

Sai dai ana gudanar da bukukuwan tunawa da Navalny a daidai lokacin da rikicin cikin gida ke ci gaba da haifar da rarrabuwar kawunan 'yan adawan Rasha, a wani yanayi da ba a taba ganin irinsa ba.

Da ma dai galibin shugabannin adawar na Rasha na gudun hijira a kasashen ketare, lamarin da ya ke rage musu karfin gogawa da Shugaba Putin wanda ya yi fice wajen murkushe masu adawa da mulkinsa.