1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwa game da garkuwa da mutane a Najeriya

Suleiman Babayo MA
March 15, 2024

Bayan garkuwa dayara, Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci ganin an yi bincike tare da hukuntan wadanda suke da hannu kan garkuwa da mutane da ake ci gaba da fuskanta a yankin arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/4diPQ
Garkuwa da mutane a Najeriya
Garkuwa da mutane a NajeriyaHoto: AP/dpa/picture alliance

A wannan Jumma'a MDD ta nuna damuwa da yadda aka samu lamarin garkuwa da mutane da dama a Najeriya da suka hada da kananan yara, tare da kira na ganin an gudanar da bincike wadanda suke haddasa irin wannan ta'asa domin gurfanar da su a gaban kotu.

Shugaban Hukumar kare hakkin dan Adam na majalisar, Volker Turk ya nuna bakin cikin yadda aka yi garkuwa da yara 'yan makaranta da sauran jama'a a ynakin arewacin Najeruiya tare da cewa bai dace haka ya zama abin da aka saba ba.