1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Houthi ta harba makami mai linzami kan jirgin ruwan Girka

January 16, 2024

Mayakan Houthi na ci gaba da zafafa hare-haren da suke kai wa kan jiragen ruwa a Bahar Maliya, da hakan ya kai su ga harba makami mai linzami kan wani jirgin ruwan kasar Girka a gabar teku a yankin Yeman.

https://p.dw.com/p/4bKrZ
Wasu mayakan Houthi dauke da makamai
Wasu mayakan Houthi dauke da makamaiHoto: Mohammed Hamoud/Anadolu/picture alliance

A cewar wani kamfanin da ke kula da zirga-zirgar jiragen ruwa  a yankin ya ce harin ya lalata wani bangare na jirgin da ke kan hanyar zuwa Isra'ila ta mashigin Suez, duk da cewar rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin dakon kayan na Girka na  ci gaba da nausawa zuwa Isra'ailan.

Ko a baya bayannan, sojin ruwan Amurka sun kakkabo wasu makamai masu linzami na mayakan Houthi da suka harba kan wani jirgin ruwan Amurka,   duk da cewa  mayakan na Houthi sun yi nasarar harba wani makami mai linzami kan wani jirgin ruwan Amurka a gabar tekun Oman.

Hukumar da ke tattara bayanan shige da ficen jiragen ruwan karkashin kulawar Burtaniya ta akwai rahoton kai hari yankin gabar arewa  maso yammacin Saleef a Yeman, duk da ba su bayar da cikakken rahoton kai harin ba.

.