1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta jaddada ci gaba da kai hare-hare

February 4, 2024

Amurka za ta ci gaba da zafafa kai hare-haren maida martani kan mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran, kamar yadda babban mashawarci Shugaba Biden kan tsaron kasar Jake Sullivan ya tabbatar a hirarsa da NBC.

https://p.dw.com/p/4c29S
Jirgin yakin Amurka da ke kai farmaki Yemen
Jirgin yakin Amurka da ke kai farmaki YemenHoto: U.S. Central Command/Handout via REUTERS

Kawancen dakarun Amurka da Burtaniya sun kaddamar da farmaki kan mayakan Houthi na Yeman, domin dakile hare-haren da mayakan ke kaiwa kan jiragen ruwan da ke shawagi a tekun Bahar Maliya da gabar tekun Aden.

Al'amura sun sake tsananta a yankin tun bayan kisan sojojin Amurka uku a Jordan a ranar 28 ga watan Janairun wannan shekara. A cewar ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, sojin na Amurka sun harba makamai masu linzami kimanin 85, a wurare 7 da ke kasancewa tungar mayakan Houthi  Siriya da Iraqi.

Sai dai kungiyar Houthin ta ce barazanar Amurka ba zai sauya musu ra'ayi ba, na goyon bayan da suke bawa al'ummar Gaza.