1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya Amnesty ta zargi sojojin kasar

Uwais Abubakar Idris AH
November 1, 2018

Kungiyar kare hakin jama’a ta Amnesty International ta ce dole ne a tuhumci sojojin Najeriya da suka yi kisan mutane 45 'yan Shi'a.

https://p.dw.com/p/37VuS
Nigeria Abuja Proteste von Schiiten des Islamic Movement
Hoto: picture-alliance/AA/A. A. Bashal

Kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International da ta bayyana bacin ranta a kan abin da ta kira kisan da ya sabawa doka da aka yi wa ‘yan Shi'a a Najeriyar, ta ce tana da shaidu da suka nuna sojojin sun yi amfani da manyan bindigogi wanda jami'anta sun gani da ido a wurare biyar da suka ziyarta a Abuja. Kiraye-kiraye na lallai sai gwamnati ta hukunta sojojin da suka aikata laifin ya sanya tunkarar rundunar sojan don jin ta bakinsu a kan lamarin, inda mukadashin kakakin rundunar tsaron Najeriyar Brigadier Janar John Agim ya bayyana cewar.

Nigeria Abuja Proteste von Schiiten des Islamic Movement
Hoto: picture-alliance/AA/A. A. Bashal

Ya ce: ''sojojin nan fa an samesu ne a bakin aikinsu mu ba za mu yi wani abu da zai cuci kungiyar ‘yan Shia ba, ai suna da mambobi har a soja, amma idan suka zo za su hargitsa zaman lafiya ba za mu sa ido ba. ''

Kafin wannan dai ‘yayan kungiyar sun bizne wasu daga cikin mutanen da aka kashe a yanayi na nuna alhini musamman ga ‘yan uwan mutanen da aka kashen. Tun daga shekara ta 2015 dai lamura na ci gaba da muni a duk lokacin da aka yi arangama tsakanin sojojin da   ‘yan Shi'a a Najeriya. Inda suka ce za su ci gaba da tatakin ne saboda  har yanzu gwamnatin Najeriya  na tsare da shugabansu Sheikh Ibrahim Zakzaky.