1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta sanar da sabon kunshin tallafi ga Ukraine

June 7, 2024

Shugaban Joe Biden na Amirka ya nemi afuwar takwaransa na Ukraine kan jinkirin da majalisa ta yi na amincewa da kunshin tallafi ga Ukraine.

https://p.dw.com/p/4gn88
Shugaban Amirka, Joe Biden da takwaransa na Ukraine, Volodmyr Zelensky
Shugaban Amirka, Joe Biden da takwaransa na Ukraine, Volodmyr ZelenskyHoto: Evan Vucci/AP Photo/picture alliance

Shugaba Joe Biden a ranar Juma'ar ya kuma sanar da cewa, zai sanya hannu kan sabon kunshin tallafi ga Ukraine na dala miliyan 225, domin ta sake gina cibiyar wutar lantarkinta.

Karin bayani: Amirka ta amince da bai wa Ukraine tallafin yaki

Wannan dai ita ce ganawa ta gaba da gaba ta farko da shugabanin biyu suka yi tun bayan da Shugaba Zelenky ya kai ziyara a birnin Washington a watan Disambar shekarar 2023.

Ana sa ran shugabannin za su sake haduwa a mako mai zuwa a taron koli na kasashe masu karfin arzikin masana'antu na G-7 da zai gudana a kasar Italiya, yayin da shugabanin kasashen yammacin Turai ke tattaunawa kan amfani da kadarorin Rasha da suka rike bayan da ta kaddamar da mamaya a Ukraine, domin samawar wa Kyiv tallafin dala biliyan 50.