1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta yi barazanar ci gaba da fada da Ukraine

Suleiman Babayo AH
July 12, 2023

Kungiyar tsraon NATO/OTAN ta yi alkawarin tabbatar da kare iyakokin kasashen mambobinta tare da kara taimako ga kasar Ukraine saboda kutse daga Rasha.

https://p.dw.com/p/4Tkox
Lithuania | Taron kasashen kungiyar NATO
Shugabannin kungiyar tsaron NATO lokacin taro a LithuaniaHoto: Kacper Pempel/Reuters

Ana sa ran a karshen taron kungiyar tsaron NATO/OTAN da ke gudana a kasar Lithuania kasashen Yamma za su samar da manufa ta dogon lokaci kan taimakon kasar Ukraine wadda take fuskantar kutse daga Rasha. Tun farko Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya yi zaton samun lokaci da za a kayyade na shigar kasar kungiyar NATO, amma haka bai yuwu ba.

Shugabannin kasashe 31 mambobin kungiyar ta NATO sun tattauna kan batutuwan tsaro da sabunta alkawarin kai dauki kan duk kasar da take bukata, gami da kashe kudin da aka amince a fannin tsaro. Kana wani abinda ya fito fili shi ne kara yawan sojoji a iyakar kungiyar ta NATO da kasar Rasha wadda ake gani tana barazanar tsaro ga wasu kasashen mambobin kawancen NATO.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce kasarsa za ta ci gaba da fafatawa da Ukraine a fagen-daga muddin kasashen Yammacin Duniya suka ci gaba da shirin neman ganin bayan kasar Rasha. Ministan ya fadi haka a wata hira da wata jaridar kasar Indonesiya da aka wallafa a wannan Laraba.

Lavrov ya ce kasashen Yamma karkashin Amirka na nemna ganin sun mamaye komai a duniya. Shi dai ministan harkokin wajen na Rasha Sergei Lavrov yana kan hanyar halartan taron kasashen gabashin nahiyar Asiya aa birnin Jakarta na Indonesiya inda ake sa ran shi ma Antony Blinken Sakataren harkokin wajen Amirka zai halarci taron.