1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kiilace babban asibitin Gaza

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 15, 2023

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar agaji ta Red Cross sun nuna fargaba tare da bukatar a kare dubban marasa lafiya da fararen hula, bayan da sojojin Isra'ila suka mamaye asibitin Al-Shifa.

https://p.dw.com/p/4Yq67
Isra'ila | Al-Schifa | Zirin Gaza | Hamas
Sojojin Isra'ila, a harabar asibitin Al-Shifa na yankin Zirin GazaHoto: Israeli Defence Forces/REUTERS

Sojojin Isra'ilan dai sun kai samame asibitin na Al-Shifa da ke zaman mafi girma a yankin Zirin Gazan, inda suka ce suna farautar mayakan Hamas ne da ke da maboyar karkashin kasa suka fake a rigar masara lafiya da fararen hular da ke neman mafaka a asibitin. A nasa bangaren shugaban Hukumar Bayar da Agajin Jin-Kai ta Majalisar Dinkin Duniyar Martin Griffiths ya bayyana fargaba kan mamaye asibitin na Al-Shifa a shafinsa na X cewa ko kuma Twitter.