1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka ta Kudu

ANC na shirin kafa gwamnatin hadaka

Binta Aliyu Zurmi LMJ
June 2, 2024

Babbar jam'iyyar adawa a kasar Afirka ta Kudu Democratic Alliance DA, ta samar da tawagar da za ta jagoranci zaman tattaunawa da sauran jam'iyyun kasar domin kafa da gwamnatin hadaka.

https://p.dw.com/p/4gYHr
Afirka ta Kudu | Shugaban  Kasa | Cyril Ramaphosa | ANC | Zabe
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril RamaphosaHoto: Jerome Delay/AP/dpa/picture alliance

A karon farko jam'iyya mai mulki ta ANC ta rasa rinjaye a zaben da ya gudana, bayan kwashe shekaru 30 tana jan akalar kasar. Shugaba Cyril Ramaphosa da sauran shugabannin jam'iyyun adawa sun halarci zauren da Hukumar Zabe ta sanar da sakamakon a hukumance, sai dai jam'iyyar tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudun Jacob Zuma ta yi fatali da sakamakon da ta bayyana da haramtacce. Sai dai a nasa bangaren shugaban jam'iyyar DA wacce ta zo ta biyu a zaben, John Steenhuisen ya ce, a shirye suke su tunkari duk kalubalen da zai taso. Ana dai tsammanin DA din da EFF ne jam'iyyu na farko da ANC za ta nemi kafa gwamnatin hadaka da su, duk kuwa da cewa akwai yiwuwar tuntubar MK ta tsohon shugaban kasar Zuma.