Matasan Afirka sun fara neman mafita
August 17, 2021Matasan dai sun gudanar da taron ne, da nufin tatauna ire-iren kalubalén da suke cin karo da su a wanan yanayi da duniya ke fama da ta'addanci da sauyin yanayi da ma uwa uba batun kiwon lafiya a lokacin ga da ake fama da annobar COVID- 19. Matasan daga kasashen Mali da Senégal da Najeriya da Cote d'ivoire da Togo da Guinéa da Benin da Burkina Faso da kuma Nijar mai masaukin baki, sun kuma tatauna kan hanyoyin samo mafita kan wadannan kalubalai da ke gabansu wadanda ke hana rayuwarsu ci-gaba.
Matasan dai kan fara kowace rana da wakoki da rawar gargajiya da ma motsa jiki, kafin fara tatunawar. Birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar din ne dai yakarbi bakuncin Matasan Scout din na Afirka, inda suka sharé mako guda suna sada zumunci da hadin kai a tsakaninsu. Zeinabou Ali matashiya ce da ta fito daga jihar Maradi, ta kuma ce bayan sada zumunci ta samu darasi kan zamantakewa. Aminu Mukhtar Wudil ma'aikacin gwamnati ne daga Najeriya da kuma ya kasance tela, kira ya yi ga 'yan uwansa matasa da su tashi tsaye su nemi da sana'o'i koda suna aikin gwamnati, kasancewar a yanzu an samu karuwar larurori na rayuwa da albashi kadai ba zai ishe su ba.