1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'addanci a Afirka cikin jaridun Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
June 23, 2023

Jaridun Jamus sun mayar da hankali a kan halin da ake ciki a Yuganda da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Sudan da siyasar Najeriya da noma a Saliyo a wannan makon.

https://p.dw.com/p/4SzBV
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Yuganda | ADF | IS
Sojojin Yuganda da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, na yakar ADFHoto: Alain Uaykani/Xinhua/picture alliance

Za mu fara ne da sharhin da die tageszeitung ta wallafa mai taken "Hadin gambizar IS domin yada ta'addanci a Tsakiyar Afirka." Ta ce masu tsaurin ra'ayin addini kama daga Somaliya zuwa Afirka ta Kudu sun sake karfafa ayyukan kungiyar 'yan ta'addan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango wato ADF. Wannan yana bayyane ne a cikin sabon rahoton kwararru da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar. Jaridar ta ce wasu masu kaifin kishin addini na kasashen Afirka baki daya na samar da tallafin kudi da kuma dabaru ga kungiyar ADF ta Yuganda da ke da alhakin kashe-kashe a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Hasali ma, masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun nuna yadda 'yan tawayen na Yuganda suke ba ni gishiri in ba ka manda da wasu kungiyoyin da ke da'awar jihadi kamar Ahlul Sunna wal-Jama'a ta Mozambik da al-Shabaab ta Somaliya. die tageszeitung ta bayyana yawan kudin da wadannan kungiyoyin 'yan ta'adda ke musanyawa, inda ta ce tsakanin 2019 da 2020 kawai suka yi amfani da tsarin musayar kudi na Islama mai suna hawala wajen jigilar Dala 400,000 daga Somaliya tare da ratsawa Yuganda da Habasha da Kenya kafin su isa hannayen 'yan kungiyar ADF.

Sudan | Khartum | Darfur | Yaki
Ci gaba da barin wuta a kasar SudanHoto: REUTERS

Ita kuwa Frankfurter Allgemeine Zeitung, a  sharhinta mai taken "Fada ya sake tsananta a Sudan." Ta ce jim kadan bayan karshen mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta na 11 tun bayan fara yakin, an koma luguden wuta da manyan bindigogi tare da fito na fito a kan titunan Khartoum tsakanin sojojin gwamnati da wadanda ke biyayya ga Janar Hamdane Daglo. Haka kuma ake samun kazamin fada a wasu yankuna na kasar musamman yankin Darfur, wanda ya shafe shekaru 20 yana fuskantar yakin basasa. Jaridar ta ce mutane da yawa sun tsere daga Darfur zuwa Chadi, yayin da dama suka mutu baya ga matan da aka yi wa fyade. Da ma gwamnan Darfur Minni Minnawi ya yi kira ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ICC, ta gudanar da bincike kan karuwar tashe-tashen hankula a Darfur.

Najeriya| Bola Tinubu
Sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Ita kuwa Zeit Online ta mayar da hankali kan Najeriya, inda ta yi shagube tana mai cewa "Yaki da cin-hanci da rashawa ya yi awon gaba da shugaban yaki da yi wa tattalin arziki zakon kasa." Jaridar ta ce bayan dakatarwa da kama gwamnan babban bankin Najeriya, wato Godwin Emefiele sabon shugaban Tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi wani sabon yunkuri a yaki da cin-hanci da karbar rashawa. Sai dai a wannan karon ruwan ya ci shugaban Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa EFCC Abdulrasheed Bawa mai shekaru 43 a duniya, wanda shi ma ke hannu jami'an DSS. Zeit Online ta dasa ayar tambaya game da wannan manufa, inda ta ce ko Tinubu ya fara yaki da bata-gari da ke hana ruwa gudu a fannin bunkasa tattalin arziki ne ko kuma wani salo ne na raba gari da manyan jami'ai da suka yi aiki karkashin magabacinsa Muhammadu Buhari? Lokaci ne zai bayar da damar tantance dan duma da kabewa.

Saliyo | Shugaban Kasa | Julius Maada Bio
Shugaban kasar Saliyo Julius Maada BioHoto: Ali Balikci/AA/picture alliance

A nata bangaren die tageszeitung ta tabo batun da ta danganta da "Mamayar filayen noma a Saliyo", inda ta ce kasar ta yammacin Afirka na da arzikin ma'adinai da kasar noma mai albarka da ke jan hankalin masu zuba jari na kasashen waje. Sai dai jaridar ta ce wannan tsari ya zame wa masu karamin karfi ci-gaban mai hakan rijiya, saboda sun bayar da kasarsu haya na shekaru da yawa amma ya zama hasara a gare su daga bisani. Sai dai gwamnatin Saliyo na nenam canza wannan al'amari. Jaridar ta ce sababbin dokoki biyu sun kare koken 'yan kasa domin hana kwace musu gonaki. Sannan sun tanadi fadin gona da ba zai wuce hekta dubu 15 da za a iya bayarwa haya ga 'yan kasuwa masu zuba jari ba. Wani abu da jaridar die tageszeitung ta nuna a matsayin ci-gaba shi ne, yadda za a samar wa mata filayen noma a matakin daidaiton jinsi da karfafa musu gwiwa saboda sun kasance ginshikin noma a Saliyo din.