1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
August 14, 2020

Baatun yanke hukuncin kisa a Kano da ke Najeriya da harin da aka kai a gandun daji a Nijar da kuma siyasar Yuganda, sun dauki hankulan jaridun Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/3gz60
Niger Giraffen-Park Koure
Harin ta'addanci a gandun dajin Koure da ke Jamhuriyar NijarHoto: AFP/S. Ag Anara

A wannan mako za mu fara sharhin jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka Jamhuriyar Nijar, tana mai cewa hari na kisa a gandun dajin rakuman dawa a karshen mako. Ta ce kwana guda bayan kisan gillar da aka yi wa wasu Faransawa shida ma'aikatan wata kungiyar agaji da 'yan Nijar biyu da ke yi musu rakiya, an tsananta bincike domin gano wadanda ke da hannu a wannan ta'asa. Sojoji da ke samun tallafi daga jiragen saman yakin Faransa sun bazu a dajin mai nisan tafiyar sa'a guda da mota daga Yamai fadar wamnatin Nijar din. Jaridar ta ce ya zuwa tsakiyar wannan mako ba wata kungiya da ta dauki alhakin kisan mutanen. Kungiyar nan da ke da'awar kare addinin Musulunci da Musulmi baki daya, ta fito ta musanta hannu a harin. Sai dai an fi kyautata zaton cewa kungiyar Boko Haram ko takwararta ta IS ne suka aikata ta'asar. Gandun dajin da ke a yankin Kouré na da matukar farin jini ga 'yan yawon bude ido duk da barazanar rashin tsaro da ake fuskanta a yankin.
A hannun shari'ar Musulunci wannan shi ne taken labarin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga game da hukuncin kisa da wata kotun shari'a da ke Kano ta yanke wa wani matashi kuma mawaki Yahaya Sharif-Aminu bisa zargin yin kalaman batanci ga addinin Musulunci, bayan wani baiti da ake zargin ya watsa ta kafar sadarwa ta Whatsapp, inda a ciki ya yi kalaman batanci ga Annabi Mohammad (SAW). Jaridar ta ce hukuncin kisan ya haskaka yadda sau da yawa ake amfani da hukunce-hukunce masu tsauri na Islama a Tarayyar Najeriya musamman ma arewacin kasar. Jaridar ta kara da cewa matashin dan shekaru 22 a duniya wanda kamin a kama shi ba wani sananne ba ne a Najeriyar, bai musanta zargin ba. Ba a dai sani ba ko za a aiwatar da hukuncin, domin dole sai ya samu sahalewar gwamnan jihar Kano, amma sau da yawa gwamnonin jihohin Najeriya na dari-darin sanya hannu kan aiwatar da hukuncin kisa.

Nigeria Kano Justiz Hisbah
Jami'in Hukumar Hisba a jihar Kano daga tsakiyaHoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar
Uganda Kampala Bobi Wine vor Gericht
Bobi Wine a gidan kasoHoto: Katongole Abdu Hakim

Daga batun shari'a a Najeriya sai na siyasa a kasar Yuganda, inda jaridar Neues Deutschland ta labarto cewa, shahararren mawakin nan na kasar wanda kuma ake wa lakabi da Bobi Wine ya tayar da hankalin mahukunta. Ta ce shugaban kasa na tsawon shekaru, Yoweri Museveni wanda kuma a badi zai nemi wa'adin mulki karo na shida, na kara fuskantar babban kalubale bayan da mawakin ya kafa wata sabuwar jam'iyyar siyasa National Unity Platform wato NUP, da zai mata jagora ta kalubalanci Museveni a zaben shekarar 2021. Shekaru 34 ke nan Museveni na shugabantar kasar ta Yuganda. Bobi Wine wanda sunansa na yanka shi ne Robert Kyagulanyi Ssentamu ya bayyana kafuwar sabuwar jam'iyyar tasa da muhimmin mataki a gwagwarmayar 'yantar da 'yan kasar daga mulkin kama karya na Shugaba Museveni da jam'iyyarsa ta National Resistance Movement wato NRM a takaice.