Adesina ya sake zama shugaban bakin AFDB
August 27, 2020Talla
Adesina mai shekaru 60 da ke zama tsohon ministan noma a tarayyar Najeriya ya sami kaso dari cikin dari na kuri'un da aka jefa daga dukkanin bankunan mambobin yanki da ma wadanda ba na yankin ba.
A shekarar 2015 ce Adesina ya zama dan Najeriya na farko da ya fara rike shugabancin wannan bankin da ke zama na biyar a jerin manyan cibiyoyin kudi na duniya masu ba da bashi.
Sabon wa'adin zai fara ne daya ga watan Satumba.