1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta kamo fursunonin Kuje da suka tsere

Uwais Abubakar Idris ZUD/AS
August 24, 2022

Bayan kwashe fiye da wata guda ana neman su, wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan kason babban birnin Najeriya, Abuja, sun shiga hannun hukuma.

https://p.dw.com/p/4Fzrl
Nigeria I Ausbruch Hochsicherheitsgefängnis in Kuje
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gabatar da wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje a farkon watan Yulin da ya gabata.

A yayin da take nuna wa 'yan Najeriya fursunonin da ta yi nasarar sake kamowa, rundunar ta 'yan sandar, ta kuma gabatar da wasu masu garkuwa da mutane da fashin da makami da yawansu ya kai 21 a Abuja tare da makamansu. DSP Mustapha Bello Abdulkadir, wani jami'i a rundunar 'yan sandan Najeriyar ya shaida wa DW cewa sun samu wadanda ake zargin da miyagun makamai.

An dai kamo fursunonin da masu garkuwa da mutanen a jihohin  Kaduna da Naija da Nasarawa da Filato da kuma Edo.