Abubuwan ban sha'awa a gasar AFCON ta 2023
Côte d'voire mai masaukin baki ta lashe gasar cin kofin kasashen Afirka bayan doke Najeriya 2 da 1 a wasan karshe. Abin da ya saka suka zama na farko da suka karfi bakunci da suka samu nasarar gasar tun shekara ta 2006.
Gagarumin bikin budewa
Gasar AFCON ta 2023, an bude da hada launuka da muryoyi gami da wakokin kasar Côte d'Ivoire. An ga nasara da rashin nasara, da wasu labarai gami da korar masu horas da 'yan wasa, an kuma jefa kwallaye na tarihi a raga.
Rungumar kaddara
Ga kasar Côte d'Ivoire mai masaukin baki ta fara da rasa wasanni biyu a matakin farko na rukunin A - inda kasar Equatorial Guinea ta doke Côte d'Ivoire 4 da 0. Ita dai Côte d'Ivoire ta kare a matsayi na uku a matakin rukuni. Lokacin da suka samu labarin tsallakawa zuwa mataki na gaba, har sun sallami mai horas da 'yan wasan kasar Jean-Louis Gasset.
Makabartar masu horas da 'yan wasa
Kamar yadda ake cewa, ana saukar da korar masu horas da 'yan wasa. Abin da ya faru a Côte d'Ivoire ba a taba gani ba, inda aka sallami masu horas da 'yan wasa takwas, sannan daya ba za a tsawaita kwantiraginsa ba. Rui Vitoria dan kasar Potugal mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Masar na cikin wadanda aka sallama bayan rasa wasa a zagaye na biyu.
Muhimmin sauyi lokacin gasar
Duk lokacin da kungiya ko kasa ta sallami mai horas da 'yan wasa, ana sa ran samun sauyi na gajeran lokaci. Amma zai iya nuna abin da zai biyo baya? Bayan Côte d'Ivoire ta iya tsallakawa zuwa matakin na gaba, an maye gurbin Jean-Louis da mataimakinsa Emerse Fae (wanda hotonsa yake sama) wanda a baya yake da kwarewa na horas da 'yan wasa. Abin da ya biyo baya ya zama tahiri.
Wani abu na farko: Mace alkali
Bouchra Karboubi ba ta zama mace ta farko alkalin wasa a gasar AFCON ba. Amma Salima Mukansanga 'yar kasar Ruwanda ce a shekara ta 2022. Sai dai a wannan gasar AFCON, ita Bouchra Karboubi ''yan kasar Maroko ta zama ta farko daga yankin arewacin Afirka na Larabawa da ta yi alkalancin wasa a rukunin A tsakanin Guinea Bissau da Najeriya.
Launukan tutoci na magoya baya
Magoya baya a gasar cin kofin Afirka kowani lokaci suna sanye da launuka na kasashe kuma haka lamarin ya kasance a filayen wasa. Magoyan bayan Senegal sun nuna takaicin yadda masu dauke da kofin suka gaza wuce zagaye na biyu.
Gwarzon wasan kusa da na kusa da na karshe
Mai tsaron gidan kasar Afirka ta Kudu Ronwen Williams ya tare bugun daga kai sai mai tsaron gida hudu lokacin wasa da Cape Verde, bayan tashi wasa babu wadda ta jefa kwallo a raga. Mothobi Mvala ya jefa kwallon da ta tabbatar Afirka ta Kudu ta kai wasan kusa da na karshe, karon farko tun shekara ta 2000.
Murna duk da rashin nasara
Duk da rasa wasa da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na kusa da na karshe, magoya bayan Cape Verde ba su nuna kasala ba a gasar ta AFCON. Kamar Equatorial Guinea sun ba da mamaki wajen wuce matakin rukuni, kuma lokacin da 'yan Cape Verrde suka koma gida sun samu gagarumar tarba.
Jefa kwallo a raga na 'yan Najeriya
Williams bai nuna siddabaru ba lokacin wasan kusa da na karshe da Afirka ta Kudu ba, abin da ya kai zuwa bugun daga kai sai mai tsaron gida da Najeriya. Gwarzon Afirka na shekara Victor Osimhen kuma dan wasan Najeriya gami da Ademola Lookman da kuma William Troost-Ekong suka nuna tasiri.
Labarin farfado da Najeriya
Najeriya ta kai wasan karshe tare da jinjina ga mai horas da 'yan wasan Jose Peseiro. Dan shekaru 63 da haihuwa dan kasar Potugal ya fuskanci suka lokacin da Najeriya ta tashi 1 da 1 da kasar Equatorial Guinea a wasan farko na AFCON. Daga Peseiro ya sauya abubuwa tare da kara karfin tsaron gida inda Najeriya ta kai wasan karshe.
Samun sa'a na Côte d'Ivoire
Duk da Sebastian Haller ya yi yunkuri, amma akwai sa'a. Dan wasan gaba wanda ya warke daga cutar sankara bayan dadewa ba ya wasa ga kungiyar Dortmund a gasar Bundesliga. Sannan Sebastian Haller bai yi wasanni da dama a gasar AFCON ba saboda jin ciwo. Amma ya jefa kwallo ta karshe da ta kai Côte d'Ivoire lashe gasar baki daya.
Zama gwarzo
Ba a bukatar sa'a, amma Sebastien Haller ya jefa kwallo ana mintoci na 81 a wasan karshen lokacin da Cote d'Ivoire a shiga gaban Najeriya a gasra AFCON. Kuma da wannan kwallo magoya bayan kasar suka bazama kan tituna bisa nasarar da suka samu.