Ɗan sandan Afghanistan ya harbe dakarun NATO huɗu
September 16, 2012Ana zargin wani jami'in ɗan sandan Afghanistan da kissar wasu dakaru huɗu na ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO da ke aiki a ƙasar ta Afghanistan, abin da ƙawancen da Amirkar ke jagoranta ke cewar shi ne karo na biyu cikin kwanaki biyu a jere da wani jami'in tsaron Afghanistan ke kissar takwarorin aikinsa na yammacin duniya.
Adadin sojojin ƙetaren da jami'an tsaron gwamnatin Afghanistan suka kashe daga farkon wannan shekarar dai ya kai 51, abin da kuma ke yin barazana ga shirin da ƙungiyar ƙawancen tsaron ke yi na bai wa jami'an tsaron Afghanistan horo, domin ɗaukar alhakin lamuran tsaron ƙasar yayin da dakarun na NATO suka kammala ficewa a shekara ta 2014.
Ko da shike rundunar ƙasa da ƙasa ta ISAF da ke yaƙi a Afghanistan ba ta yi cikakken bayani game da lamarin ba, amma ta ce ya afku ne a yankin kudancin ƙasar ta Afghanistan a wannan Lahadin.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas