1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɗan adawa ya zargi shugabar Laberiya da yunƙurin kissa

November 8, 2011

Taƙaddamar siyasa a Laberiya yana ɗaukar sabon salo a yayin da al'ummar ƙasar ke kammala jefa ƙuri'ar zaɓen shugaban ƙasa

https://p.dw.com/p/1374e
Winston Tubman da shugaba Ellen Johnson Sirleaf na LaberiyaHoto: AP/Montage:DW

Babban abokin hamayyar shugaba Ellen Johnson Sirleaf, wanda kuma ya janye daga takarar a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar daya gudana a wannan Talatar, ya zargi dakarun tsaron shugaba Sirleaf da ƙoƙarin kashe shi a lokacin da suka buɗe wuta akan wani gangamin 'yan adawar daya gudana a jejiberin ranar zaɓen na Laberiya. A cewar Winston Tubman cikin zantawar da yayi tare da manema labarai, lokacin daya yi ƙoƙarin ficewa daga motar sa a wajen gangamin ne wani matashi ya tilasta masa komawa cikin motar, inda kuma yace yayi amannar wani harsashin bindigar da aka nufi harbe shi ne yayi sanadiyyar mutuwar matashin. Ya ce ya yi amannar jami'an 'yan Sandan suna bin umarnin hukumomin ƙasar ta Laberiya ne, inda ya ce umarnin kuwa shi ne a kawar dashi daga ban ƙasa.

A halin da ake ciki kuma, zaɓen shugaban ƙasar Laberiya da aka sanya ran zai ƙarfafa tsarin dimoƙraɗiyya a ƙasar, ya fuskanci ƙarancin masu jefa ƙuri'a a wannan Talatar, bayan da abokin karawar shugaban ƙasar ya janye daga zaɓen - ana dab da yinsa, tare da yin watsi da kiraye-kirayen da kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Amirka suka yi masa. Ɗaukar matakin dai zai baiwa shugaba Johnson Sirleaf dake zama mace ta farko dake riƙe muƙamin shugaban ƙasa a ɗaukacin nahiyar Afirka damar lashe zaɓen. Sai dai kuma masu sanya ido akan zaɓen da kuma ƙwararru, na da ra'ayin cewar rashin fitowar masu zaɓe da yawa ka iya yin ƙafar ungulu ga halaccin gwamnatin ta da kuma dasa ayar tambaya akan nasarar ta ta.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu