1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɗan adawa ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Zambiya

September 23, 2011

A karo na huɗu jagoran 'yan adawa a Zambiya Michael Sata da ya daɗe yana sukar kasancewar China a ƙasar, ya sake tsayawa takarar neman shugabancin ƙasar kuma yayi nasara.

https://p.dw.com/p/12fVm
Michael Sata, mutumin da ya lashe zaɓen shugaban ƙasar ZambiyaHoto: AP

A rahotonta jaridar Tageszeitung waiwaye ta yi kan aikin haƙo tagulla a Zambiya tana mai cewa China ta shiga ƙasar ne lokacin da wannan harka ta rushe sakamakon faɗuwar farashin tagulla wanda ya janyo ficewar kamfanonin ƙasashen yamma daga ƙasar. Ta ce China dai ta ƙirƙiro da sabbin guraben aiki sannan ta farfaɗo da aikin haƙo tagulla, to amma ta yi baƙin jini a tsakanin talakawa saboda albashinta ya kasa na ƙarancin albashin da hukuma ta tsara kana kuma ƙa'idojin aiki a kamfanonin China ba su kai matsayin na duniya ba. Saboda haka ake yawaita yajin aiki da bore amma cinikaiya tsakanin Zambiya da China na ƙara bunƙasa.

Taƙaddama game da angizon China a Zambiya, inji jaridar Neues Deutschland tana mai kwatanta zaɓen shugaban ƙasar na ranar Talata da zama wani hukunci na so ko adawa da ɗinbim masu zuba jari na China a ƙasar. Da babbar tazara China ce ke kan gaba wajen zuba jari a Zambiya mai arzikin tagulla. Jaridar ta ce babu wata ƙasa a Afirka da China ke da angizo kuma aka buɗe mata ƙofofi kamar Zambiya, saboda manufofin siyasa na shugaba mai barin gado Rupiah Banda.

Äthiopien Meles Zenawi
Firaministan Ethiopia Meles ZenawiHoto: AP

Amirka na gina sansanin ajiye jiragen sama marasa matuƙa a Ethiopia sannan za ta ƙarfafa aiki a tsibiran Seychelles da Djibuti a wani mataki na yaƙi da ta'adda da masu fashin jirgin ruwa. A rahoton da ta rubuta akan wannan batu jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce tun kimanin shekaru huɗu da suka gabata Amirka ta fara tattaunawa da gwamnatin Ethiopia amma hukumomi a birnin Addis Ababa sun ɗauki tsawon lokaci kafin su miƙa kai. Ethiopia na ba wa Amirka cikakken haɗin kai a yaƙi da 'yan ta'adda a gabashin Afirka. Sai dai kamar yadda ake gani a yankunan da ake amfani da irin waɗannan jiragen saman yaƙi maras matuƙa, sau da yawa ba 'yan ta'adda ne kaɗai ake halakawa ba, a'a fararen hula ma rasa rayukansu.

Flüchtlinge Kurdufan Sudan
'Yan gudun hijira akan iyakar arewaci da kudancin SudanHoto: picture alliance/dpa

Kwan gaba kwan baya inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai nuni da dangantakar siyasa tsakanin arewaci da kudancin Sudan. To amma bisa ga dukkan alamu an samu ci-gaba a 'yan kwanakin nan biyo bayan sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar da nufin warware rikicin kan iyaka dake tsakaninsu. To sai dai duk da haka Jaridar ta ce bisa la'akari da matakan da gwamnati a birnin Khartoum ke ɗauka da nufin ƙarfafa bin dokokin addinin Islama a ɓangarenta na kan iyakar, to ba abin mamaki ba ne idan waɗannan matakan suka sake rura wutar rikicin kan iyakar tsakanin ƙasashen biyu, domin masu adawa a yankin sun ce dalilin faɗan da suke yi shi ne danniya da girmar kai da gwamnatin Khartoum ke nunawa wadda kuma har wa yau ba ta amincewa da kafa wata ƙasa mai bin tsarin jam'iyu da yawa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullhai Tanko Bala