Ɓarkewar Cutar murar tsuntsaye a China
December 31, 2011Jami'an kiwon lafiya sun ruwaito sake ɓarkewar cutar murar tsuntsaye a kasar ta China, a karon farko da aka samu kwayoyin cutar a jikin bil'adama cikin watanni 18. Rahotanni sun ce a san samu kwayoyin cutar ta H5N1 ne a jikin wani matukin motar pasinja a garin Shenzhen mai cunkoson jama'a dake yankin kudancin China. Garin na Shenzhen mai yawan al'umma miliyan 10, na kan iyakar China da Hong kong ne. Honkong dai ta killace dubban kaji da dangoginsu, tare da haramta shigar da dangogin tsuntsaye cikin kasar, tun bayan samu kwayoyin cutar murar tsuntsayen ta H5N1a jikin kaji uku, a tsakiyar watan Disamban nan mai karewa.Duk da cewar cutar tana da mummunar lahani, hukumar kula da lafiya ta Majalisar Ɗunkin Duniya ta nunar da cewar babu barazanar yaɗuwar kwayoyin cutar tsakanin mutane, da ɓarkewarta a 2003. A yanzu haka dai hukumomin China da Hong Kong na aiki kafaɗa da kafaɗa domin shawo kan matsalar.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman shehu Usman