1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙuri'ar raba Gardama tsakanin Al'umma a Girka

November 1, 2011

Firaministan Girka ya sanar da buƙatar yin ƙuri'ar raba gardama akan yarjejeniyar da ƙasar sa ta cimma da ƙungiyar Tarayyar Turai

https://p.dw.com/p/1337c
Hoto: dapd

Firaministan ƙasar Girka George Papendreau ya yi ƙira da a gudanar da ƙuri'ar raba gardama game da yarjejeniyar da ƙasar ta cimma tare da tarayyar Turai a makon daya gabata, wadda kuma ta sanya yafewa ƙasar kusan kaso ɗaya cikin ukku na yawan bashin dake kanta, tare da yi mata alƙawarin samun wani rancen daya kai na kuɗi Euro miliyan dubu 130. Papendreau ya shaidawa majalisar dokokin ƙasar Girka cewar, batun na da muhimmamcin daya kamata a baiwa al'ummar Girka damar tofa albarkacin bakin su akansa. Sai dai mutane da dama sun yi mamakin wannan sanarwar. Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'ar da aka gudanar dai ya nunar da cewar mafi rinjayen 'yan Girka basu ɗauki yarjejeniyar da kyakkyawar manufa ba. Ana kuma ganin ka'ɗa ƙuri'a akan batun ka iya ruruta wutar rashin tabbas game da gungun ƙasashen Turai dake yin amfani da takardar kuɗin Euro ta bai ɗaya. Jerin matakan tsuke bakin aljihun da gwamnatin Papendreau take aiwatarwa a ƙasar domin cin gajiyar tallafin kasa da ƙasa dai ba su sami karɓuwa a tsakanin 'yan ƙasar ba, inda suke ta gudanar da yaje-yajen aiki da kuma zanga-zangar nuna adawa da rage kasafin kuɗin ƙasar da kuma

ƙara musu haraji. 

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakae

Edita          : Yahouza Sadissou Madobi