1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙuri'a kan shirin tsuƙe bakin aljihun Girka

June 29, 2011

Ranar Laraba 29 ga watan Yuni majalisar dokokin Girka za ta kaɗa ƙuria kan shirin tsuƙe bakin aljihun gwamnati da ke fuskantar adawa daga al'uma

https://p.dw.com/p/11lh3
Tutar Girka a hannun ɗan zanga-zanga a gaban 'yan tsaron ginin majalisaHoto: AP

Yau, 29 ga watan Yuni 'yan majalisar dokokin ƙasar Girka ke jefa ƙuri'a domin samun sabon tallafi na euro milyan dubu 28 domin taimaka wa shirinta na tsuƙe bakin aljihu. Ana buƙatar kaɗa wannan ƙuri'ar ne domin share fagen bai wa ƙasar da bashi ya yi wa katutu ƙarin tallafi na euro miliyan dubu 12. A cikin wani jawabi da ta yi bayan zaɓar ta a matsayin sabuwar shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF, Christine Lagarde ta jaddada buƙatar gaggauta sa hannu kan wannan shiri.

Matakan tsuƙe bakin aljihun na Girka dai sun ci karo da zazzafar adawa daga al'umar ƙasar. A Athens babban birnin ƙasar an yi taho mu gama tsakanin 'yan sanda da 'yan zanga-zanga a lokacin da dubban ma'aikata da suka shiga yajin aiki suka yi jerin gwano zuwa ginin majalisar dokoki. 'Yan zanga zanga guda uku da 'yan sanda 21 sun samu raunuka bayan da 'yan sanda suka yi amfani da gas mai sa hawaye domin tarwatsa jama'a. An kuma samu ɓarkewar sabon faɗa da safiyar Laraba 29 ga watan Yuni a gaban ginin majalisar dokokin ƙasar.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu