Ƙungiyar ƙasahen larabawa na ƙara fuskantar matsin lamba
January 21, 2012Ƙungiyar ƙasashen larabawa na shirin ƙara tsawaita wa'adin tagawar wakilanta a ƙasar Siriya da wata guda duk da irin matsin lambar da take fuskatan.Sakamakon yadda ake yin suka dangane da yadda tawagar ta kasa dakatar da zubar da jinin da ake yi a ƙasar Siriya kusan watannin goma da suka wucce.
Nan gaba ne aka shirya shugaban tawagar ta masu saka ido akan siriya Mohammed Ahmed Moustafa -Al -Dabi zai gabatar da wani bahasi a birin Alƙahira wanda akan sa ne ƙungiyar za ta yanke shawara akan ci-gaban aikin tawagar. Kamfanin dillanci labarai na Faransa AFP ya ambato wani jami'in ƙungiyar Ali Jarouh ya na mai cewar za a ƙara tsaiwata lokacin da wata guda saboda wata ɗaya bai isa tawagar ta kammala aikinta ba .
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala