1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar AU ta ɗage taronta daga Malawi

June 12, 2012

Tarayyar Afrika AU, ta ɗage zamanta daga ƙasar Malawi ya zuwa Adis Ababa. kasancewar ta yi barazanar cafke shugaban ƙasar Sudan Omar Hassan Al Bashir da zaran ya jefa kafa

https://p.dw.com/p/15Cub
epa03084113 A handout image made available by the South African Government Communication and Information System (GCIS) shows a general view of the the new African Union building where the present 26th meeting of the NEPAD Heads of State and Government Orientation Committee (HSGOC) is being held, Addis Ababa, Ethiopia, 29 January 2012. EPA/Jacoline Prinsloo / GCIS / HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES
Shugabanin AfirkaHoto: picture-alliance/dpa

Ƙungiyar Tarayyar Afrika, wato AU ta dage zaman taronta da zata gudanarwa a nan gaba a cikin watan Yuli mai zuwa daga ƙasar Malawi ya zuwa kasar Habasha wato a birnin Adis Ababa.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne tun bayan da kasar ta Malawi ta ɗauki alƙawarin cafke shugaban ƙasar Sudan Omar Hassan Al Bashir da zaran ya jefa kafa a ƙasar domin ta mutunta sammacin da kotun kasa da kasa ta ICC ta bada a kan shi tun a shekara ta 2009.

Ministan harakokin wajen kasar ta Sudan ya ce wannan wata alama ce da ke tabbatar da irin nasarorin da suke samu a duniya bisa ga makarkeshiyar kotun ta ICC.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi