1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin samun maslaha a rikicin Siriya

June 16, 2013

Birtaniya ta ce ita da Rasha za su iya ajiye banbancin ra'ayoyi da su ke da shi kan Siriya, su ɗauki matakin da zai kawo ƙarshen rikicin ya kuma kyautata rayuwar talakawan ƙasar.

https://p.dw.com/p/18qqc
Britain's Prime Minister David Cameron (R) greets Russia's President Vladimir Putin in Downing Street, in central London June 16, 2013. The two leaders will meet ahead of the G8 summit in Northern Ireland, amid local media speculation that they will discuss the crisis in Syria. REUTERS/Luke MacGregor (BRITAIN - Tags: POLITICS)
Cameron da PutinHoto: Reuters

Rasha da ƙasashen yamma za su iya kawar da banbance-banbancen da ke tsakaninsu dangane da rikicin Siriya, kalaman Firaministan Birtaniya ke nan David Cameron bayan da suka yi tattaunawar share fagen taron ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi na G8, tare da shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin.

Cameron ya ce taƙaddmar da ke tsakanin Birtaniya da Rasha kan Siriya ba sirri ba ne, amma a yanzu haka, akwai inda ra'ayoyinsu ya zo daidai kuma shi ne halin da talakawan ƙasar ke ciki, haɗe da cewa sun ga irin haɗarin da ke tattare da ɗaukar matakai masu tsauri, kuma idan har suka haɗa kai suka kuma mai da hankali kan wannan batu, babu shakka za su cimma nasara.

Shi ma shugaba Putin ya amince da cewa taron na G8 shi ne kaɗai matakin da ya fi dacewa wajen sassanta rikicin na Siriya, saboda rikici ne wanda mataki na diplomasiyya ne kaɗai zai iya ciyo kan shi.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar