1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen yamma sun fito zahiri sai shugaban Siriya ya kau

August 18, 2011

Shugabannin ƙasahen Turai da Amirka suka ce duk wata tattaunawa a Siriya bata da amfani, illa shugaba Assad da a dole ya miƙa mulki.

https://p.dw.com/p/12JHp
Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy da Shugaban Siriya Bashar al-Assad, lokacin da ake ɗasawaHoto: AP

Ƙasar Amurka da ƙungiyar Tarayyar Turai sun yi kira ga shugaban Siriya Bashar al-Assad da lallai ya sauka daga mulki.

Da ta ke yin kiran sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton, ta ce irin matsayin da shugaba Assad ya ɗauka na murƙushe masu adawa da shi, ya sanya ƙimarsa ta zube a idanun duniya.

A na ta ɓangaren sakatariyar harkokin ketare ta ƙungiyar EU Catherine Ashton ta bayyana cewar ƙungiyar ta EU na nan ta na shirye-shiryen ƙara ƙaƙabawa gwamnatin Assad takunkumi.

Su ma dai ƙasahen Birtaniya da Jamus da Faransa irin wannan kira su ka yi inda su ka kara da cewar lokaci ya yi da ya kamata shugaban ya fuskanci gaskiya.

Tun da fari dai shugaba Assad ya shaidawa sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon, cewar dakarunsa sun tsagaita karawar da suke yi da 'yan adawa, sai dai bayanan dake fitowa daga kasar ta Siriya na nunin cewar an sake kashe mutane da kuma kame wasu da dama a garin Latakia.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Mohammad Abubakar