1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen larabawa sun yin Allah wadai da Siriya

September 6, 2012

Shugaban ƙasar Masar Mohamed Mursi ya yi kira ga gwamnatin shugaba Bashar Al Assad da ta yi marabus

https://p.dw.com/p/164In
Arab foreign ministers attend a meeting at the Arab League headquarters in Cairo, September 5, 2012. REUTERS/Asmaa Waguih (EGYPT - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Shugaban ya baiyana haka ne a wajan taron ƙungiyar ƙasashen larabawa da ke ci gaba da gudana a birni Alƙahira na Masar, wanda taron kuma ya yi Allah wadai da kisan gilar da gwamnatin ke aiwatar wa a Siriyar.

Gidajan telbijan na duniya sun nuna hoton kujerar Siriya a zauran taron wanda babu wakilin ƙasar a zaune a kan ta, wanda ko a can baya kusan wata guda da ya gabata wakilin na Siriya a ƙungiyar ta ƙasashen larabawa ya ci gaba da wakiltar ƙasar sa.Wannan dai wani abu ne da ke nuna yadda ƙasar ta Siriya ke zama saniyar ware a cikin ƙasashen duniya, sakamakon yadda gwamnatin ta Bashar Al-Assad ke ci gaba da yin kunnen ƙashi a kan kiraye kirayen da ƙasashen duniyar suke yi na ta dakatar da kisan farar hular da sojojin gwamnatin ke yi.

Ƙasashen larabawa sun dage sai an sami canji a Siriya

A lokacin da ya ke magana a gaban wakilan na ƙungiyar ƙasashen larabawa shugaba Mursi ya ce tilas ne shugaba Assad ya yi marabus.Ya ce ''gwamnatin Siriya har yanzu ta na da sukunin dakatar da zubar da jini, ya ce ya kammata sun yanke shawara a daidai lokacin da ya dace kafin lokaci ya ƙure''.Wannan dai shi ne karo na farko da wani shugaban na ƙungiyar ƙasashen larabawa da ke yin kira ga takwaran sa da ya ajiye aikin shugabancin .Ƙungiyar ta buƙaci kwamitin sulhu na MDD da ya yi yunƙurin irin wanda ya yi a ƙasar Libiya na amfanin da ƙarfin sojan da ya kawo ƙarshen tsohuwar gwamnatin.

Egypt's President Mohamed Mursi talks at the Arab League headquarters in Cairo September 5, 2012. Mursi, promising to put Cairo back at the heart of Arab affairs, made an impassioned appeal to Arab states on Wednesday to work for an end to the bloodshed in Syria and said the time had come to change the Syrian government. REUTERS/Egyptian Presidency/Handout (EGYPT - Tags: POLITICS) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Taron ƙungiyar ƙasashen larabawa a birnin Alƙahira na MasarHoto: Reuters

Damuwa ƙasashen a kan halin da jama'ar ƙasar Siriya suke ciki

Halin da ake ciki yanzu haka a ƙasar ta Siriya inda sama da mutane dubu ɗari suka ficce a cikin watan jiya zuwa ƙasashen maƙofta kamar yadda hukumar yan gudun hijira ta MMD ta baiyana ya kiɗimar da ƙasashen larabawan.Shugaban ƙasar Masar ɗin Mohamed Mursi wanda wannan shi ne karo na farko da ya ke yin jawabi a gaban taron ƙungiyar tun bayan da aka zaɓe shi a kan matsayin na shugaba; ya ce za a kafa wani kwamiti na shiga tsakanin na ƙasa da ƙasa waɗanda suka hada da Iran da Turkiya da Saudiyya da kuma Masar domin samar bakin zaren rikicin,kuma ya sha alwashin cewar zasu kawo sauyi a cikin ƙasashen larabawa.Ya ce ''Juyin juya halin da Masar ta yi ;ya ce ba wai kwai ba, na samar da yanci ne, da walwala na al'ummar ƙasar ba kaɗai; ya ce abu ne da zai zama jagora har ga sauran ƙasashen na larabawa''.

Syrian refugees are seen at the Za'atri refugee camp in the Jordanian city of Mafraq, near the border with Syria August 30, 2012. The U.N. refugee agency (UNHCR) said on Tuesday the pace of Syrian refugees reaching Za'atri camp in northern Jordan had doubled, with 10,200 arriving in the last week, heralding what could be a bigger movement. REUTERS/Majed Jaber (JORDAN - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
'Yan gudun hijira na Siriya a JordanHoto: Reuters

Sauyi dai ko da ƙarfi da alama ' yan addawa na Siriyar sun dage sai ya samu. Kuma a kwai rahotanin da ke nuna cewar a ƙasar ta Masar a gaban ofishin jakadancin Siriya an yi taho mu gama tsakanin jam'ian tsaro da yan addawar; na Siriya masu neman canza tutar ƙasar a ofishin da tutar juyin juya hali.

Mawallafi : Blaschke Björn/Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto