1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

290212 EU-Gipfel

Usman ShehuMarch 1, 2012

Shugabannin Tarayyar Turai sun buɗe wani taron da ake ganin shine zai ɗau ƙwararan matakai na shawo kan rugujewar tattalin arzikinsu asashen

https://p.dw.com/p/14Ccx
Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU, hinten, 5.v.l.) steht am Montag (30.01.12) bei einem Fototermin waehrend des EU-Gipfels in Bruessel (Belgien) zum sogenannten Familienfoto neben weiteren Teilnehmern. Merkel hat sich gegen einen Sparkommissar fuer Griechenland ausgesprochen. "Ich glaube, dass wir eine Diskussion fuehren, die wir nicht fuehren sollten", sagte sie am Montag vor dem EU-Gipfel in Bruessel. Es gehe darum, Griechenland zu unterstuetzen. "Ich moechte keine kontroverse Diskussion, sondern eine erfolgreiche", sagte sie. Ueber Griechenland werde auf dem Gipfel nicht viel gesprochen, denn die Troika sei noch in Athen und die Gespraeche mit den Banken ueber den Schuldenschnitt seien noch nicht abgeschlossen. (zu dapd-Text) Foto: Torsten Silz/dapd
EU Gipfel 2012 BrüsselHoto: dapd

Tun lokacin da ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro suka shiga matsalar tattalin arziki, kusan ko wane taron da shugabannin ƙasashen ke yi, babu abinda ke mamaye shi, illa batun ceto ƙasashen da suka yi kusan durƙushewa. Sai dai a wannan karon shugaban hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso, ya yi ƙoƙarin nuna wa yan jarida cewa akwai sakel, inda yace akwai batun Girka taron, amma batun sauye-sauye a kasafin kuɗaɗen ƙasashen Tarayyar Turai shine zai kasance gaba a taron da shugabannin suka buɗe a birnin Brussels.

"Batare da yin ƙarin gishiri ba, ina ganin zamu iya gamsuwa, mun fara ɗaukar ingantattun matakai da za su kai ƙasar Girka gaci. Don haka ina tsammanin wannan taron ƙasashen EU zai banbanta da waɗanɗa suka gabata."

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) und der Praesident der Europaeischen Kommission, Jose Manuel Barroso, unterhalten sich am Montag (30.01.12) bei einem Fototermin waehrend des EU-Gipfels in Bruessel (Belgien). Merkel hat sich gegen einen Sparkommissar fuer Griechenland ausgesprochen. "Ich glaube, dass wir eine Diskussion fuehren, die wir nicht fuehren sollten", sagte sie am Montag vor dem EU-Gipfel in Bruessel. Es gehe darum, Griechenland zu unterstuetzen. "Ich moechte keine kontroverse Diskussion, sondern eine erfolgreiche", sagte sie. Ueber Griechenland werde auf dem Gipfel nicht viel gesprochen, denn die Troika sei noch in Athen und die Gespraeche mit den Banken ueber den Schuldenschnitt seien noch nicht abgeschlossen. (zu dapd-Text) Foto: Torsten Silz/dapd
EU Gipfel 2012 BrüsselHoto: dapd

Manufar Taron

A wannan taron shine dai ba'a fayyace tsarin da shugabannin suka shirya faɗa ba, aksarin shugabannin na son sanyya hannu kan matakan ceto tattalin arziki da suke ɗauka a lokacin taron. A kan batun da ya shafi ƙasar Girka dai, kusan shugabannin sun fara fidda wani tsammanin, domin arzikin ƙasar sai ƙara rugujewa yake yi, yan ƙasar da ke adawa da shirin tallafin sai ƙara bazuwa suke a titinu suna bore. Abinda kuma ya ƙara kawo shakka a zukatan shuganiin ƙasashen dake bada tallafi. A jawabinda ya yi gaban majalisar dokin Girka, shugaban majalisar dokokin Tarayyar Turai Martin Schulz cewa ya yi.

"Abinda ƙasashen EU ke fatan gani shine, wata alama ta haɗin kai, da yanci, haɓakar demokraɗiyya da ci gaba. Tutar Tarayyar Turai buƙatar ta ɗaya ne ga ko wace ƙasa. Don haka an zuba ido bawai ga nan Girka kaɗai ba, harda sauran ƙasashen Tarayyar Turai"

Riot police grapple with a demonstrator during protests against planned reforms by Greece's coalition government in Athens, February 10, 2012. REUTERS/Yiorgos Karahalis (GREECE - Tags: BUSINESS EMPLOYMENT CIVIL UNREST POLITICS)
Yan sandan Girka ke karawa da masu boreHoto: Reuters

Fiddan tsammani kan Girka

A matsayin sa na dan ƙasar Jamus, shugaban majalisar dokokin Tarayyar Turai, Schulz yana ganin sannu a hankalin dangantakar ƙasashen Jamus da Girka ta na rugujewa.

"Wannan tattalin arzikin zamani a Turai, yana barin kashi 40 cikin ɗari na matasa a rashin aikin yi. Wannan kuwa ba shine kadai bangaren da ya shafa ba, amma harga tsarin demokradiyya a Turai"

Yanzu haka dai babban ƙalubalen dake kagaban ƙasashen Tarayyar Turai shine su inganta fannin ilimi, zuba jari da samar da makashin da baya gurbata mahalli. Amma batun ceto tattalin arzikin ƙasashen ya kankane duk irin wannan mahimman abubuwa da ake buƙata. Sai dai kwamishinan kuɗi na EU Olli Rehn cewa ya yi

Shigar Sabiya cikin EU

"Mu a hukmar EU muna ganin ya zama dole, mu tabbatar da haɓaka tattalin arzikin ƙasashen dake amfani da Euro, mu shawo kan matsalolin da muke fiskanta, domin sake farfadowa"

Serbia's President (L) and European Commission President Jose Manuel Barroso (R) hold a joint news conference after a meeting in Brussels February 28, 2012. Romania threatened on Tuesday to derail European Union plans to grant Serbia membership candidate status in a row over minority rights in the former Yugoslav state, EU diplomats said. REUTERS/Eric Vidal (BELGIUM - Tags: POLITICS)
Boris Tadic shugaban asar Sabiya da Jose Manuel Barroso shugaban hukumar EUHoto: Reuters

Ɗaya daga abinda ke cikin jadawalin taron dai shine, batun shigar da ƙasar Sabiya a ƙungiyar EU, bayan da suka warware batun ƙasar Kosovo, sai dai adawan da Romeniya ta nuna ya kawo cikas. Amma ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerlle cewa ya yi.

"Kosovo da Sabiya sun cika ƙa'idar da muka shinfiɗa. Don haka yana da mahimmanci a matsayinmu don cika alƙawarin da maka yi"

Ana saran shugabannin EU za su taɓo batun ƙasar Siriya inda za su yi ƙira ga MDD ta sauke nauyin dake kanta na kare al'ummar Siriya, kana batun agazawa ƙasashen arewacin Afirka da aka yi juyin-juya hali, shima zai shiga jadawalin.

Mawallafa:Christoph Hasselbach/Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu