1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen duniya na ƙara matsa ƙaimi kan Siriya

August 23, 2011

Amurka da wasu sauran ƙasashen Turai na shirin gabatar da wani ƙudiri akan Siriya a gaban ƙwamitin sulhu na Majalisar Dinikin Duniya

https://p.dw.com/p/12LeJ
Shugaban ƙasar Siriya Bashar-Al- AssadHoto: dapd

Amurka da wasu ƙasashen Turai guda fuɗu na shirin gabatar da wani ƙudiri ga ƙwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya;domin saka takunkumi ga shugaba Bachar Al Assad na Siriya da kuma wasu sauran muƙaraban sa.

Ƙudirin wanda ƙasashen Amurkan da Faransa da Jamus da kuma Ingila zasu gabatar,zai bada damar ɗaukar mataki ga kotun duniya da ke hukumta miyagun laifufukan yaƙi akan cin zarafi da kuma kisa da sojojin gwamnatin ƙasar Siriya suka aikata kan masu zanga zangar ƙin jinin gwamnati.Kawo yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane dubu biyu da ɗari biyu suka rasa rayukan su a sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi a ƙasar ta Siriya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita :Umaru Aliyu