1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen Duniya na ci gaba da amincewa da Majalisar riko ta Libiya

April 4, 2011

Ƙasahen Italiya da kuwait sun bada goyon baya ga Majalisar riƙon ƙwarya ta wucin gadi a ƙasar Libiya

https://p.dw.com/p/10nRo
Ministan waje na riko Ali al-Essawi.Hoto: dapd

Ƙasar Kuwait ta ce nan gaba za ta bada sanarwa amincewa da majalisar riƙon ƙwarya ta ƙasar Libiya wadda 'yan tawaye ke jagoran ta. Ministan harkokin waje na ƙasar Sheikh Mohammed Al Salem Sabah wanda ya ce tuni sun amince da majalisar a tsakanin su, ya ce a cikin ƙwanaki na gaba za su baiyana sanarwa a hukumce. Kuwait ta kasance ƙasa ta biyu a cikin ƙasahen larabawa bayan Qatar da ta amince da Majalisar.

Tun da fari dai Kasahen Faransa da kuma Italiya daga Bisani suka yarda da kwamiti Franco frattini ministan Harkokin waje na Italiyar, ya ce sun yarda da wannan sabuwar majalisa da za ta kasance wadda za ta riƙa magana da suna sabuwar gwamnatin Libiya wacce kuma za su yi hulda da ita. A makon gobe ne ƙwamitin ƙasahen dake tuntuɓar juna akan rikicin na Libiya zai gudanar da wani taro a birnin Doha na Qatar kamar yadda ministan harkokin wajen na ƙasar Ingila William Hague ya baiyana

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Zainab Mohammed Abubakar