1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙaruwar 'yan gudun hijira daga Siriya

August 15, 2012

Yaƙin basasan da ake yi a ƙasar Siriya tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye ya haddasa kwararar 'yan gudun hijira a ciki da wajen ƙasar.

https://p.dw.com/p/15pru
Zeltlager Za’atari an der jordanische Grenze – Schutzplane für syrische Flüchtlinge. Vor Hitze und Sandstürmen verlassen die Flüchtlinge ihre überhitzten Zelte und suchen frische Luft unter Schutzplanen, 06.05.2012. Zulieferung am 15.8.2012. Fotograf/ Copyright: Doris Bulau
Hoto: Doris Bulau

Dubban 'yan gudun hijirar ƙasar Iraƙi dake cikin ƙasar ta Siriya na daga cikin waɗanda ke tsere wa yaƙin zuwa ƙasarsu inda a nan ma babu tabbas, wato kenan suna ƙaura daga wani bala'i zuwa wani. Mohammad Nasiru Awal na ɗauke da ƙarin bayani.

Kimamin shekaru biyar da suka wuce faɗace-faɗace da hare haren bam da na ƙunar baƙin wake sun zama ruwan dare a Iraƙi, wadda ta kasance ƙarƙashin ayyukan tarzoma, rikicin ƙabilanci da na addini, abin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 1500 a kowane wata. Wannan rikicin ya tilasta wa miliyoyin mutane yin ƙaura a cikin Iraƙi da kuma ƙasashe maƙwabta. Kimanin 'yan Iraƙi dubu 500 suka tsere zuwa Jordan sannan miliyan ɗaya zuwa Siriya.

Zeltlager Za’atari an der jordanische Grenze – Mutter Um Achmad im Lager Za’tari. Die Mutter Um Achmad ist verzweifelt und beklagt die Sandstürme, 06.05.2012. Zulieferung am 15.8.2012. Fotograf / Copyright: Doris Bulau
Hoto: Doris Bulau

A shekarun baya bayan nan gwamnatin Iraƙi ta yi ta ƙoƙarin ganin 'yasn ƙasar sun koma gida, inda take ba da lada ga waɗanda suka koma gida don raɗin kansu. Amma wa zai yi sha'awar komawa gida cikin ruɗani, rashin aikin yi da muhimmin ababan more rayuwa, bayan yana samun dala 200 da gidan kwana kyauta, hasken wutar lantarki da ruwan sha daga hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Siriya? Sai dai rikicin Siriyar a yanzu ya sa a dole 'yan gudun hijirar Iraƙi sun fara yi wa kansu kiyamun laili, suna komawa gida cikin wannan ruɗani, kamar yadda wannan mutane ya nunar.

Ya ce: "Zan koma Iraƙi ne idan ƙasar ta samu kwanciyar hankali, kuma ba na fuskantar wata barazana, kuma da fatan iyali na za su rayu cikin kwanciyar hankali da lumana."

Zama cikin zaman laiya da lumana har yanzu na zaman wani mafalki a Iraƙi. A watan da ya gabata mutane 325 suka rasu sakamakon tashe tashen hankula, adadi mafi yawa cikin shekaru biyu. A rana guda ɗaya a cikin watan Yuli mutane 100 suka kwanta dama a hare hare a faɗin ƙasar. Sai dai a cikin makonni uku mutane dubu 22 sun sake ƙaura daga Siriya wadda rigingimun da take fuskanta ya tunasar da su halin da suka taɓa shiga ciki a Iraƙi, inji Ahmed Abu Maryam wani ɗan gudun hijirar Iraƙi.

Zeltlager Za’atari an der jordanische Grenze – Kinderspielplatz. Kleiner Spielplatz für die Kinder im Lager Za’atari, 06.05.2012. Zulieferung am 15.8.2012. Fotograf / Copyright: Doris Bulau
Hoto: Doris Bulau

Ya ce: "Na kwashe shekaru kimanin 15 a Siriya, amma tun kwanaki 10 da suka wuce na koma birnin Bagadaza. Ana cikin mummunan hali a can, ba tsaro ba taimako, ba aikin yi. A Iraƙi ma ba tsaro ɗari bisa ɗari, amma ya fi lokutan baya."

Ita ma wannan matar 'yar Iraƙi da ta tsere daga rikin na Siriya cewa ta yi.

Ta ce: "Mun je Siriya a shekarar 2009 lokacin da Iraƙi ta shiga mummunan hali. Amma yanzu mun koma gida, ƙasar mu ce, abubuwa sun fara kyautatuwa. Muna yi wa 'yan Siriya fatan alheri."

Idan za a kwatanta da yaƙin basasa a Siriya, ga da yawa daga cikin mutanen da suka koma gida, Iraƙi na kan hanyar samu kyakkyawar makoma. A halin da ake ciki gwamnati a birnin Bagadaza ta yi kira ga dukkan 'yan gudun hijirar Iraƙi da su koma gida.

Mawallafi: Mohammed Nasir Awal
Edita : Zainab Mohammed Abubakar