1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Euro-Gruppe Abschluss

May 17, 2011

Ministocin kula da harkokin kuɗi na ƙasashen sun ɗauki kwanaki biyu suna tattauna matsalolin koma bayan tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/11IJg
Jean-Claude TrichetHoto: dapd

Shugaban ƙungiyar Ministocin kula da harkokin kuɗi na gungun ƙasashen dake anfani da takardar kuɗi ta Euro, Jean-Claude Junker, ya buƙaci ƙasar Girka ta sake fasalin bashin dake kanta - muddin tana buƙatar ƙara samun ɗauki domin farfaɗo da tattalin arziƙin ta.

Ministocin kula da harkokin kuɗi na ƙasashen dake yin amfani da takardar kuɗi ta Euro, waɗanda suka kwashe tsawon kwanaki biyu suna gudanar da taron haɗin gwiwa a tsakanin su da asusun bayar da lamuni a duniya na IMF a birnin Brussels na ƙasar Beljiam, sun tattauna matsalolin koma bayan tattalin arziƙin da wasu ƙasashen Turai kamar Girka da kuma Portugal ke fama da ita, tare da yin ƙira ga ƙasar ta Portugal ta ƙara yin namijin ƙoƙari wajen samar da sauye-sauyen tattalin arziƙin da za su bata sukunin ƙara samun ɗauki daga ƙasashe takwarorin ta a Turai, waɗanda ke yi´n amfani da takardar Euro.

Shugaban ƙunigiyar ministocin kuɗi, wanda kuma shi ne firaministan ƙasar Luxembourg Jean-Claude Junker ya faɗi- a wajen taron cewar tilas ne ƙasashen dake fama da kariyar tattalin arziƙin su faɗaɗa sauye-sauyen da suka samarwa:

EU Finanzministertreffen in Ungarn Olli Rehn
Hoto: picture alliance/dpa

"Zan jaddada cewar babu wanda yake adawa da zaɓi ɗaya tilo na buƙatar faɗaɗa sauye-sauyen da ƙasashen ke samarwa. Ba zan fitar da batun bin takameimei tsarin yin kwaskwarima ga tsarin basussukan dake ƙasashen ba, amma wannan bashi ne zai warware matsalar ba. Idan har su cika waɗannan sharuɗɗan, to anan ne za mu yi maganar sake fasalin bashin, amma tilas ne su fara ɗaukar ingantattun matakai gabannin mu fara maganar sake fasalin bashin."

A cewar shugaban ƙungiyar ministocin ƙasashe 17 dake yin anfani da takardar kuɗin Euro, Girka ba ta da wani zaɓin daya wuce ta nemo kuɗi Euro miliyan dubu 50 daga shirin sayar da kanfanonin gwamnati da kuma hannayen jarinta domin biyan bashin dake kanta, wanda yakai kimasnin kashi 150 cikin 100 na yawan abubuwan da ƙasar ke samarwa.

Shi ma a lokacin da yake tsokaci game da ɗaukin da wasu ƙasashen Turai ke nema domin farfaɗo da tattalin arziƙin su, kwamishinan kula da harkokin kuɗi da kuma tattalin arziƙi na ƙungiyar tarayyar Turai Olli Rehn, cewa yayi ya zama wajibi su ɗauki wasu matakai tukuna:

"Har yanzu akwai giɓin da za'a cike musamman abinda ya fashi ƙarfafa buƙatar aiwatar da kasafin kuɗi sau da kafa da kuma sayar da hannayen jarin gwamnati, tilas ne ƙasar Girka ta ƙara yin huɓɓasa wajen aiwatar da kasafin kuɗin ta na shekara shekara da kuma irin sauye-sauyen da take samarwa."

Tuni dama wata tawagar ƙwararru daga ƙungiyar tarayyar Turai take gudanar da binciken gano ko sauye-sauyen da ƙasar Girka ke aiwatar wa suna haifar da sakamako mai kyau, binciken da kuma muƙaddashin ministan kula da harkokin kuɗi na Jamus Joerg Asmussen ya ce akwai yiwuwar ƙarawa tawagar wasu kwanaki akan wa'adin aikin su dake cika a wannan Larabar.

Brüssel EU Olli Rehn
Olli RehnHoto: picture-alliance/dpa

Sai dai kuma akwai fargabar cewar idan har ƙungiyar ta amince da sake fasalin bashin da ake bin Girka, to kuwa ƙasashen Portugal da Ireland waɗanda su ma suka ci gajiyar ɗauki daga shirin tallafin gaggawa na ƙungiyar tarayyar Turai da kuma asusun IMF zau sake nazarin basussukan dake kansu, ko da shike kuma tuni ƙasar Ireland ke neman a rage mata yawan kuɗin ruwan da take biya, bisa hujjar cewar ƙa'idojin da aka gindaya mata suna ƙara jefa ta cikin matsalar giɓin kasafin kuɗi da kuma munanna yanayin matsalar bashin da dama yayi mata kanta.

Mawallafi :Saleh Umar Saleh
Edita : Abdullahi Tanko Bala