Ƙarshen aikin tawagar masu saka ido a Siriya
August 16, 2012Ƙwamitin ya cimma wannan shawarar' ce a ƙarshen taron da ya gudanar;kuma hakan ya zo ne a daidai lokacin da sakataran majalisar Ban Ki Moon ya ke gamuwa da cikas wajan shawo kan mutumin da ake jin cewar shi ne zai maye gurbin Kofi Annan. A matsayin mai shiga tsakanin; wato tsohon ministan harkokin waje Aljeriya Lakhdar Brahimi.
A hannu ɗaya ,hukumar agaji ta ayyukan jin ƙai ta Majalisar Ɗikin Duniyar ta ce sama da mutane miliyion biyu da rabi ne ke buƙatar agajin gauggawa sakamakon tashin hankali na Siriya.Ministan harkokin waje na Faransa; wanda ya ziyarci wani sansani yan gudun hijira na ƙasar ta Sirya a Jordan inda ya ke yin ziyara; ya ce suna cikin wahala.''taimakon jin ƙai bai isa ba, kuma ya dace a samar da shi, domin za a lura cewar waɗannan mutane na mutuwa da yuwan sannan ga rashin magungunan asibiti''.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman