1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban ƙasar China a Amirka

January 18, 2011

Tattauna batun darajar takardar kuɗin Yuan dakuma hulɗa tsakanin ƙasashen biyu na daga cikin mahiman abubuwan da za a ambato a ganawar shugabannin

https://p.dw.com/p/zz1S
Sugaban China Hu JintaoHoto: AP

Shugaban ƙasar China Hu Jintao yana kan hanyar kai wata ziyarar aiki ta kwanaki ukku a ƙasar Amurka. Ziyarar wacce ta zo a daidai lokacin da ƙasashen biyu suka kasa fahimtar juna akan hulɗar ciniki, za ta bada dama ga shugabannin don tantance batun dake ciwa ƙasashen biyu tuwo a kwarya kan maganar darajar takarda kuɗin Yuan. Amirka dai na zargin ƙasar China da karya darajar takardar kuɗinta domin samun damar shigar da hajojinta

DOSSIER KOMPLETTBILD USA CHINA Besuch Hu Jintao
Shugaba Obama da Hu JintaoHoto: AP

Abinda ke ƙara haddasawa Amurkawan koma baya akan sha'anin tattalin arziki tare kuma da janyo zaman kashe wando ga al'uma. An shirya shugabannin biyu za su yi wata ganawa tare da yin taron manema labarai a fadar White House. Kafin ziyarar ta Hu Jintao wata tawagar 'yan kasuwa na ƙasar ta China da ta isa a Washington, ta sa hannu akan yarjeniyoyi na kwangiloli da aka ƙiyasta cewa sun kai euro miliyion 450.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Usman Shehu Usman