1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder zuwa Turkiya Mohammad

Nasiru AwalFebruary 18, 2004
https://p.dw.com/p/BwWN

An yi Allah wadai da kalaman da shugabar jam´iyar adawa ta CDU Angela Merkel ta yi yayin wata ziyarar da ta kai kasar Turkiya a farkon wannan mako, inda ta ce ana iya ba Turkiya wani matsayi na babbar abokiya maimakon daukar ta a matsayin cikakkiyar memba ta kungiyar tarayyar Turai EU. Yayin da yake mayar da martani game da kalaman na Merkel, FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan cewa yayi ko kadan hakan ba ta dace ba, kuma kasar sa ba ta yanke kauna game da zama memba ta kungiyar EU ba. Ita dai Merkel cewa ta yi kungiyar EU ka iya fuskantar matsalolin kudi, idan aka shigar da Turkiya a cikin ta, domin karfin tattalin arzikin wannan kasa mai yawan al´umma miliyan 70 bai kai kashi 23 cikin 100 idan aka kwatanta da na sauran kasashen kungiyar EU ba. ´Yar siyasar ta Jamus ta ce hasali ma kungiyar ta fada cikin matsalolin kudi dangane da sabbin kasashen da zata dauka a ran daya ga watan mayu. Saboda haka kamata yayi Turkiya ta zama ´yar kallo kawai, amma saboda canje-canjen da ta ke aiwatarwa, ana iya ba ta wani matsayi na babbar abokiyar hulda da kungiyar EU. To sai dai wannan wani abu ne da Turkiya ba zata amince da shi ba. Shi ma shugaban gwamnatin Jamus wanda zai fara ziyara a wannan kasa a ran 22 ga wannan wata ya san da haka. Ba dai kamar Merkel ba, ita gwamnatin hadin guiwa ta SPD da Greens na bukatar a yiwa Turkiya din adalci game da batun na shiga kungiyar EU. Wannan gwamnati dai sabanin ´yan siyasar Turai masu ra´ayin mazan jiya, ba ta ganin addinin musulunci wanda daukacin ´yan Turkiya ke bi a matsayin wani cikas ga batun shigar da wannan kasa cikin EU, hasali ma gani take hakan zai ba da damar samar da fahimtar juna tsakanin al´adu da addinai dabam-dabam. Ko da yake za´a dauki shekaru da dama kafin a shigar da Turkiya cikin EU. Amma idan gwamnatin birnin Ankara ta samu nasarar cike ka´idojin kungiyar EU, to dole kungiyar ta cika alkawarin da ta dauka na fara tattauna batun shigar da Turkiya cikinta, inji Schröder. Sannan ya kara da cewa tun kimanin shekaru 40 da suka wuce gwamnatocin Turai, musamman ma na tarayyar Jamus suke yiwa Turkiya gafara sa amma har yanzu ba ta ga kaho ba. Saboda haka bai kamata a saba alkawuran da aka yiwa wannan kasa ba, musamman a wannan lokaci da take kara aiwatar da managartan canje-canjen sisaya, tattalin arziki da kare hakkin bil Adama bisa manufar samun karbuwa a Turai. Wani abin da ya daga darajar kasar yanzu haka kuma shine shirin da ta nuna game da warware rikicin tsbirin Cyprus.