1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar shugaba Hu Jintao na Sin a Indiya da Pakistan

YAHAYA AHMEDNovember 20, 2006

Shugaba Hu Jintao na ƙasar Sin, ya fara wata ziyarar aiki a ƙasashen Indiya da Pakistan, a cikin wannan makon. A duk tsawon ziyarar tasa, ana ganin cewa shugaban na Sin zai fi ba da ƙarfi ne wajen kyautata hulɗar cinikayya tsakanin ƙasarsa da Indiya da kuma Pakistan.

https://p.dw.com/p/BtxO
Shugaba Hu Jinato
Shugaba Hu JinatoHoto: AP

Wannan shekarar ta 2006 ce ƙasashen Sin da Indiya, suka ƙaddamar tamkar shekarar inganta hulɗoɗin ƙawance tsakaninsu. Tuni dai a shagulgular da aka shirya don alamta wannan zumuncin, an yi bukukuwan al’adun gargajiya na ƙasashen biyu da ziyarce-ziyarce da tawaga daban-daban na fannin tattalin arzikin ƙasashen biyu suka kai wa juna. To ƙololuwar bukukuwan tabbatad da zumuncin ne dai ziyarar da shugaba Hu Jintao na Sin ke kai wa Indiya a wannan makon.

An dai yi ta samun hauhawar tsamari a dangantaka tsakanin ƙasashen Indiya da Sin a cikin shekaru da dama da suka wuce. A cikin shekarar 1962 ne ƙasashen biyu suka gwabza da juna a wani gajeren yaƙi, amma mai tsanani. A wannan lokacin dai, dakarun Sin sun kutsa har cikin wasu yankunan jihar Arunachal Pradesh da ke arewa maso gabashin Indiyan, inda har ila yau Sin ɗin ke ikirarin cewa wani yanki na jihar mai murabba’in kilomita dubu 90, ɓangare ne na ƙasarta.

A ganin Sujit Dutta na cibiyar nazarin al’amuran tsaro ta ƙasar Indiyan da ke birnin New Delhi dai, tuni an warware matsalar ko wace ƙasa ce ke mallakar yankin na Arunachal Pradesh. Kuma da ƙasashen biyu na sha’awar ganin an warware rikicin kan iyakar tasu, da tuni an yi hakan. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Ra’ayin Sin a kan wannan batun dai shi ne; da can, wannan babbar harabar ba ga kowa take ba. Kafin yankin ya zamo jihar arewa maso gabashin Indiya kan iyakarta da Sin, akwai gidajen ibadan mabiya addinin Budha da ke da alaƙa da Tibet. Amma ita Indiyan, a ganinta, tun 1914 ne aka yanke shawara kan wannan batun, tsakaninta da Tibet, a lokacin da Indiyan ke ƙarƙashin mulkin mallakar Ingila. Sabili da haka ne nake da ra’ayin cewa, mutanen da ke zaune a wannan yankin, ’yan ƙasar Indiya ne.“

Tun shekara ɗaya da rabi dai ke nan da Indiyan ta ƙulla wata yarjejeniya musammam ta ma’ammala da Sin. Duk ɓangarorin biyu dai na nanata muhimmanci dangantakar da ke tsakaninsu a halin yanzu, a daidai lokacin da ake ta yaɗa salon haɗayyar tattalin arzikin duniya. Haɗa kansu a wuri ɗaya, zai ba su damar cin moriyar wannan salon da janyo wa al’ummansu fa’idar da yake ƙushe da ita. Kazalika kuma zai sa su iya taimakawa wajen tabbatad da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Asiya da ma duniya baki ɗaya. Amma duk da haka, a huskar tattalin arziki, akwai sauran matsalolin da ba a kau da su ba tukuna. Har ila yau dai, ita Indiyan na ɗari-ɗari da shawarar da Sin ta bayar ta kafa wani shacin cinikayya maras shinge tsakaninsu. Dalilin haka kuwa, a ganin Hanns Hillpert, na gidauniyar kimiyya da siyasa ta nan Jamus, shi ne:-

„Watakila wannan shacin, na cinikayya maras shinge, Sin ɗin ce kawai za ta fi cin moriyarsa. Ita dai Sin tana nuna ƙwazo ƙwarai da gaske a tserereniyar sarrafa kayayyaki masu rahusa, waɗanda kuma take fita da su zuwa ƙetare. Indiya ba za ta cim mata a wannan huskar ba. Idan ko ta amince da ƙiƙiro wannan shacin, to za a wayi gari kayan Sin ɗin ne za su mamaye kasuwanninta, abin da zai gurgunta nata masana’antun.“

Daga Indiyan dai shugaba Hu Jintao, zai ci gaba da ziyararsa ne zuwa Pakistan, inda a nan ma zai shafe kwanaki uku yana tattaunawa da mahukuntan birnin Islamabad. Jami’an ƙasar Indiyan dai za su sa ido ne ƙwarai kan ziyarar ta shugaba Hu a Pakistan, saboda bayan yarjejeniyar makamashin nukiliyan da Indiyan ta ƙulla da Amirka, Sin na ganin cewa kamata ya yi ta ƙarfafa hulɗodinta da Pakistan a wannan fannin. Ana dai ta yaɗa raɗe-raɗin cewa, Pakistan da Sin na dab da sanya hannu kan wata gagarumar yarjejeniya ta cinikayya maras shinge tsakaninsu.

Hulɗoɗi tsakanin Sin da Indiya da Pakistan dai, su ne ke zayyana yadda al’amura ke tafiya a kudancin Asiya da ma nahiyar Asiyan baki ɗaya. Nan gaba ma, haka dai lamarin zai kasance. Sabili da haka ne masharhanta ke ganin cewa, wannan ziyarar ta shugaba Hu Jintao na ƙasar Sin zuwa ƙasashen biyu, tana da muhimmanci ƙwarai ga makomar yankin ma gaba ɗaya.