1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZIYARAR SAKATARIYAR HARKOKIN WAJEN AMIRKA, CONDOLEEZA RICE, A MASAR

YAHAYA AHMEDJune 21, 2005

A farkon ziyarar da ta kai wa kasar Masar, a mukaminta na sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, ta yi kira ga yi wa kafofin siyasar kasashen Larabawa kwaskwarima da kuma daukan matakai wajen yada tafarkin dimukradiyya.

https://p.dw.com/p/BvbD
Sakatariyar har kokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, yayin da take yi wa maneman labarai jawabi a Masar.
Sakatariyar har kokin wajen Amirka, Condoleeza Rice, yayin da take yi wa maneman labarai jawabi a Masar.Hoto: AP

A jawabin da ta yi wa daliban jami’ar biirnin al-kahira, a lokacin ziyararta a kasar Masar a ran litinin da ta wuce, sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice ta bayyana cewa a cikin shekaru 60 da suka wuce, kasarta ta fi mai da hankali ne kan samad da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya, yayin da ta yi sakaci da dora harsashen dimukradiyya a yankin. Amma kawo yanzu, babu abin da aka cim ma a duk bangarorin biyu. Sabili da haka ne take ganin lokaci ya zo da ya kamata Amirka ta dau matakan nuna goyon baya ga kungiyoyin da ke bin tafarkin dimukradiyya da kuma ba su tallafi don yada wannan akidar. A takaice dai, abin da Amirka ke nufi a nan shi ne, za ta janye goyon bayanta ga gwamnatoci da shugabannin kasashen yannkin da ba sa bin tafarkin dimukradiyya. Tana so ne ta dukufa wajen ganin cewa, jama’ar yankin ne za su iya tsara wa kansu makomansu da kansu.

A biranen al-kahira da Riyadh dai, wannan sabon salon daga Washington ba zai sami goyon bayan masu jan ragamar mulki a halin yanzu ba. Da can dai, abin da aka yarje a kansa a kasashen Masar da Saudiyyan shi ne, kasashen biyu ne za su kasance muhimman abokan burmin Amirka a kasashen Larabawa. Sabili da hakan ne kuma, Amirkan ba ta cewa uffan ga take hakkin dan Adam da ake yi wa al’umman wadannan kasashen. A nata ganin dai, ko me ke kalubalantar hukumomin Masar da na Saudiyyan ma, na kalubalantar maslaharta a yankin.

Shugabannin kasashen Larabawn dai sun yi ta amfani da wannan halin wajen dawwamma kan mulki, ta yi wa duk wasu masu ra’ayoyi daban danniya, tare da amincewar Amirka. Amma wannan canza salo da Washington ke yi, wato na neman bai wa al’umman yankin `yanci da kuma damar walwala da fadar albarkacin bakinsu, zai kasance wani abin fargaba ne ga mahukuntan biranen al-kahira da Riyadh. A halin yanzu dai, shugaba Mubarak, ya amince ba da sonsa ba, da shirin bai wa wani dan takara da ke hamayya da shi damar tsayawa zaben shugaban kasar da za a gudanar a cikin `yan watanni nan gaba. Duk da hakan dai, fatarsa ce ganin cewa, ya zarce da mulkin ko kuma ya mika wa dansa ragamar mulkin kasar. Dimukradiyya kam, za ta kasance cacar baka ne tukuna.

A kasar Saudiyya kuwa, lamarin daban yake. Da wuya gidan sarautar kasar, mai fa’idoji ba iyaka, ya amince da tafarkin dimukradiyya kamar yadda ake da shi a kasashen yamma. A wani matakin kwsakwarima dai, an shirya zaben majalisa da kuma na kananan hukumomi. Amma masu sukar lamiri na ganin cewa, ba za a iya kwatanta wadannan zabukan da na dimukradiyya ba.

Sai ga shi dai Washington kuma ta zo tana matsa musu lamba, kamar a wasu yankunan na Gabas Ta Tsakiyan ma, akwai tabbataccen mulki na dimukradiyya, ko kuma kamar akwai gwamnatocin da suka fi na wadannan kasashen biyu.

Abin da za a iya nuni da shi a duk yankin dai shi ne zaben da Falasdinawa suka yi, da kuma cannje-canjen da aka samu a shugabancin hukumar Falasdinun. Sai kuma zaben da aka guudanar a Iraqi a cikin wani mawuyacin hali, ban da zabukan Lebanon da Iran. Watakila saboda hakan ne, Washington ke matsa wa muhimman abokan burminta a yankin lamba, don su ma su shiga sabon salon da ke yaduwa a Gabas Ta Tsakiyan baki daya.

Amma ai ko wannan matakin na Amirka ya zo da jinkiri. Tun shekaru aru aru ne dai, kafofin islama da dama ke zarginta da daure wa shugabannin mulki kama karya na kasashen Larabawan gindi. To a yanzu, ko wane irin sakamako Amirkan ke son cim ma, a wannan sabon salon da take niyyar sarkafa wa `yan kurarta a biranen Riyadh da al-kahira ? Sai dai a jira a gani, ko da gaske sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleeza Rice take, ko kuwa cacar baka kawai mahukuntan birnin Washington ke yi don yada angizonsu a yankin. Abin fata a nan dai shi ne fafutukar Amirkan ta kasance sahihiya, wajen janyo sauyi mai inganci kuma mai ma’ana ga halin rayuwar dimbin yawan jama’a a yankin na Gabas Ta Tsakiya.