1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar' Nicolas Sarkozy a Jamus

June 17, 2011

Shugabannin biyu sun jaddada buƙatar samar da hanyoyin magance matsalar tattalin arziki na ƙasar Girka

https://p.dw.com/p/11dYg
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban ƙasar Faransa Nicolas SarkozyHoto: picture alliance/dpa

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban ƙasar Faransa Nikola Sarkozy wanda ke ziyara a birnin Berlin sun amince da samar da hanyoyin gauggawa domin taimaka wa ƙasar Girka da ta shawo kan matsalar bashin da take fama da ita wanda ya janyo wa ƙasar kariyar tattalin Arziki.

Ko da shike dukanin shugabannin biyu babu wani daga cikin su da ya baiyana lokacin da za a baiwa ƙasar Girka ɗaukin, amma sun yi amanar cewar babu makawa yin hakan shine ke zaman mafi a'alla ga ƙasashen biyu dama sauran ɗaukacin ƙasashen ƙungiyar, domin kauce wa faduwar daraja takardar kudin Euro.A taron manema labarai na haɗi gwiwa da shugabannin biyu suka gudanar dazu dazu nan , shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya baiyana cewa yarjejeniyar da za a cimma wa domin tallafa wa ƙasar ta Girka dole ne ta kasance ta bai ɗaya akan mataki har guda fuɗu .Mataki na ɗaya da na biyu ya haɗa da yadda za a duba yawan kuɗaɗen da za'a baiwa ƙasar bayan tallafin da aka ba ta a zagaye na farko. sannan kuma shugaban ya ci-gaba da cewa.

'Mataki na ukku muna son yarjejeniya akan wannan tsari tare da babban bankin tsakiya na nahiyar turai mataki na fudu shine ya kasance an ƙaddamar da agajin gauggawa du dama cewa ba a tsaida lokaci ba amma a Satumba ba zai yiwu ba haka Oktoba domin muna karshen shekara ,idan na ce da sauri to ai zaku dubu kuga yadda ya kamata ga lisafin da na yi.'

wannan ziyara da shugaban ƙasar na Faransa ya kawo a nan ƙasar ta Jamus na zaman faɗuwa ta zo daidai da zama ga shugabar gwamnatin wacce wannan al'amari na ƙasar Girka ke ci wa gwamnatin ta tuwo a ƙwarya. Wanda kuma du dama irin ra'ayoyin da jamusawan suke da shi, na yadda wasu ke gani ya na da kwai a tallafa wa ƙasar Girka, yayin da kuma wasu basu da ra'ayin haka, ta dage kan cewar ya zama wajibi akansu na fid da ƙasar daga cikin ƙangin da ta samu kan ta a ciki na durƙushe war tattalin arziki.

'muna buƙatar sabon tsari dangane da wannan hali da ƙasar Girka ta samu kan ta a ciki kuma tilas ne ƙasar Girka ta san abinda ya rataya akan wuyan ta na tabbatar mana da cikka alƙawari, kuma ko jiya na tattauna da shugaban gwamnatin ƙasar Papanderou wanda ya shaida mana cewa suna sa ne da alƙawarin.'

Magance matsalar tattalin ariki da ƙasar Girka ke fuskanta wani bada ƙwarin gwiwa ne ga takardar kuɗin Euro a kasuwanin duniya wacce a yanzu a sanadiyar wannan al'ammari, take dab da samun koma baya Nicolas Sarkozy ya jaddada cewar ba zasu yi ƙasa a gwiwa ba wajan haɓaka takardar daraja kudin na Euro.

'Euro shi ne tushen ci-gaba nahiyar Turai, kuma ya na ɗaya daga cikin shika shikan ci-gaban da muke samu don haka Faransa da Jamus za mu ci gaba da goyon bayan Euro. An shirya kuma shugabannin biyu zasu ci- gaba da tattauna wasu batutuwa na tsaro da tattalin arziki da kuma yaƙi da ta'addanci da ke zaman babbar barazana ga ƙasashen a wajan shagalin cin abinci da shugabar gwamnatin ta jamus ta shirya saboda babban bakon.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Mafdobi