1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTimor ta Gabas

Ziyarar ministar harkokin wajen Jamus a Gabas ta Tsakiya

Suleiman Babayo AH
January 5, 2024

Annalena Baerbock ministar harkokin wajen Jamus za ta fara ziyarar wasu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya zuwa kasashen Isra'ila da Masar gami da Lebanon.

https://p.dw.com/p/4atwN
Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock
Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena BaerbockHoto: Hannes P Albert/dpa/picture alliance

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock za ta kai ziyara ranar Lahadi mai zuwa Isra'ila inda wannan zai zama ziyarar ministar na hudu tun lokacin da yaki ya barke a Zirin Gaza tsakanin Isra'ila da 'yan ta'adda na kungiyar Hamas na Falasdinu.

Karin Bayani: Jamus ta damu da rikicin Isra'ila

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce ministar za ta gana da manyan jami'an gwamnatin Isra'ila lokacin ziyarar sannan Baerbock za kuma ta kai ziyara kasar Masar gami da Lebanon. Haka na zuwa lokacin da ake nuna tsoron yuwuwar rikicin tsakanin Isra'ila da Hamas zai fantsama zuwa wasu wurare a yankin Gabas ta Tsakiya.