100112 China Iran
January 10, 2012A ƙarshen mako ne dai Tehran ta ƙara sanar da shirinta na inganta sinadran Uranium a tasharta da ke Fordo, batu daya janyo martanin gargaɗi da babbar murya daga ɓangaren Amurka. Tuni dai Amurkan ta shirya sabbin takunkumi akan Iran, a daidai lokacin da ministan harkokin kuɗi Timothy Geithner ke ziyarar kwanaki biyu a ƙasar China.
China dai ta kasance ƙasa da ta fi kowace sayen Mai daga Iran, dan gane da haka ne take jan kafa a dangane da amincewa kowane mataki da ake neman dauka akan harkokin man Tehran. China na da bukatun na Makamashi mai yawan gaske, sakamakon bunkasar harkokin kasuwancinta, wanda kuma take dogaro kacokan kan Iran. Wajen kashi 11 na yawan man da China ke saye dai daga Iran yake fitowa, wanda yakai wajen kimanin Ganga dubu 560 a kowace rana. Bayan Saudi Arabia da Angola dai, Iran ce kasa ta uku dake samarwa China Mai. Dangane da hakane kaifin martanin Beijing wa Amurka yake da muhimmanci, kan kokarinta na taɓa babban Bankin Iran wadda ke tafiyar da lamuran mai..
Acewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen China Liu Weimin " ɗaukar matakan kakabawa Iran takunmi ba shine kadai zai warware wannan rikici na shirin Nukiliyarta ba". Ya kara da cewar babu matakan da zasu fi tattaunawa da tuntubar juna yin tasiri. Daura da haka babu yadda za'ayi dokokin cikin gida suyi tasiri akan na kasa da kasa. Babu dalilan yin hakan.
Ziyarar ta ministan harkokin kuɗin Amur ka Timothy Geithner a Beijing dai nada nufin tattauna matsalolin tattalin arziki da Duniya take fama dasu, da kuma karuwar damuwa dangane da shirin Nukiliyar Iran. Kazalika agendar tattaunawar zata kunshi matakan matsin lamba akan babban bankin Iran, wanda shine ke lura da dukkan kuɗaɗen shigara da kasar ke samu daga albarkatun Mai da ake fitarwa waje. A talatar nan ce Geithner ya gana da mataimakin shugaban ƙasa Wang Qishan, yayinda zai gana da shugaba Wen Jiabao da jami'an harkokin kudi na Chinan a ranar laraba.
China dai bata yi imanin cewar harkokin nukiliyar Iran nada babbar barazana kamar yadda Amurka da ƙasashen yammaci ke nunarwa ba, sai dai akwai bukatar magabatan Tehran su dada fitowa fili wajen nunarwa Duniya cewar, ba da wata muguwar manufa suke inganta sinadaran Atom ba, sai dai kawai domin wadata al'ummar ƙasar da makamashi mai inganci.
Li Guofu ƙwararre ne kan Iran a cibiyar nazarin lamuran ƙasa da ƙasa dake birnin Beijing, wanda ya ce " matsayin China a bayyana yake, muna adawa da shirin kera makamin Nukiliya a ɓangaren Iran, amma a matsayinta na membar hukumar kula da makamashi ta ƙasa da ƙasa kuma wadda ta sanya hannu akan yarjejeniyar haramta yaɗuwar makaman nukiliya, Iran ta na da 'yancin samarwa da ƙasar ta ingantaccen makamashi na Nukiliya. Duk da cewar rahotan hukumar IAEA na bayan nan na zarginta da kera makamai, babu wata shaida a rahotan dake tabbatar da hakan".
To sai dai sakamakon wannan yanayi da ake ciki, kasar ta China na takatsantsan dangane da harkokin kasuwancinta ta Iran. Rahotannin kafofin yada labarun ƙasar ta China na nuni da cewar, kampanonin mai na Beijing sun fara rage zuba jari a Iran, kazalika an rage yawan man da ake shigowa dashi data Tehran ɗin.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal