1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Merkel a yankin gabas ta tsakiya

Hauwa Abubakar AjejeFebruary 6, 2007

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana ci gaba da ziyararta zuwa yankin gabas ta tsakiya inda a yau take isa Dubai domin tattaunawa da shugabanin yankin musamman akan batun rikicin yankin gabas ta tsakiya.

https://p.dw.com/p/BtwM
Merkel da Hosni Mubarak
Merkel da Hosni MubarakHoto: AP

Wannan ziyara da Merkel ta fara tun ranar asabar inda ta farad a zuwa kasashen Masar da saudiya,ta kaita kuma zuwa Abu Dhabi,inda nan take ta shiga tattaunawa da shugaban kasar ta hadaddiyar daular larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan kan batutuwa da suka shafi karfafa dangantakun tattalin arziki.

Merkel tana mai fatar ganin an karfafa huldar tattalin arzikin tsaknin turai da kasashen larabawa,inda ake sa ran nan bada jimawa ba zaa samarda yarjejeniyar ciniki tsakanin KTT da manyan kasashen larabawa 6.

Hakazalika an shirya wata ganawa cikin watan Afrilu, tsakanin kantoman kula da harkokin ciniki na KTT Peter Mandelson da ministocin muhimman kasashen 6n wadanda suka hada da Bahrain da Qatar;Kuwait,Oman,Saudiya da haddadiyar daular larabawa.

Merkel a matsayinta ta shugabar kasar Jamus dake rike da shugabancin KTT tace kungiyar zatayi iyaka kokarinta wajen nuna goyon bayanta ga sasanta tsakanin kungiyoyin Hamas da Fatah a yankin Palasdinawa.

“ya kamata kasashen duniya su aika masu da sako na hadin gwiwa,dake kunshe da fatan ganin an samu kasashe guda biyu yantattau,wato israila da Palasdinu kuma masu cin gashin kansu tare da zaman lafiya tsakaninsu.”

Merkel tace KTT ta fara tattaunawa da bangarorin biyu game da samarda gwamnatin Hadaka tare da batun samarda kasashe 2 na Israila da Palasdinu masu makwabtaka da juna.

Shugabar ta jamus ta kuma yi kira ga kasar Syria data amince da kasancewar kasar Israila tana mai suka gareta da laifin rashin bada hadaden hadin kanta ga shirin zaman lafiya na YGTT.

Tace kasashe da dama basa son ganin an kawo karshen rikici a YGTT

“akawai alummomi da dama daga nan turai da sauran kasashen duniya da suke adawa da wannan shiri namu na wanzar da zaman lafiya a YGTT,musamman ma dai abinda ya shafi batun nukiliya na Iran”

Kasashen larabawa a nasu bangare sun bukaci kasashen turai da kawayensu dasu dauki tsauraran mataki akan Iran game da shirinta na nukiliya.

Merkel tace kasashen larabawa suna da matukar fatar ganin cewa KTT zata bukaci Iran da tabi dokokin kasa da kasa game da shirin nata.

Daga Dubai merkel zata wuce zuwa kasar Kuwait a matsayin wani bangare na ziyarar tata tare da nufininganta dangantaku tsakanin Jamus da kasashen yankin da kuma farafado da shirin zaman lafiya na YGTT.