Ziyarar Merkel a Birtaniya
November 25, 2005Talla
Tarayyar Jamus da Birtaniya sun kuduri aniyar fadada ba juna hadin kai. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da FM Birtaniya Tony Blair suka sanar da haka a wata ziyarar aiki ta farko da Merkel ta kaiwa birnin London a matsayinta na sabuwar shugabar gwamnatin Jamus. Shugabannin biyu sun yi alkawarin maido da tuntubar juna a kai a kai, wanda aka dakatar tun a shekarar 1998. Merkel ta ce zata yi duk iya kokarin shawo kan Birtaniya mai shugabantar kungiyar tarayyar Turai a yanzu don gano bakin zaren warware takaddamar kasafin kundin kungiyar. Merkel ta ce za´a yi haka ne bisa la´akari da manufofin kowace kasa membar EU din.