1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Merkel a Amirka

June 7, 2011

Shugabar gwammnatin Jamus ta isa birnin Washington domin karɓar lambar girmamawa

https://p.dw.com/p/11VYp
Obama tare da Merkel bayan cin abincin dare a Georgetown na Amirka ranar Litinin ( 06.06. 2011).Hoto: dapd

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta isa birnin Washington, fadar gwamnatin Amirka domin ziyarar aiki ta yini biyu, wadda a lokacin ne kuma za ta karɓi lambar girmamawa ta shugaban ƙasa akan 'yanci. Za'a dai gudanar da shagalin miƙa mata kyautar ce yayin cin abincin dare a fadar shugaban Amirka ta White House a wannan Talatar.

A halin da ake ciki kuma, Merkel, tare da wasu ministoci biyar na gwamnatin Jamus dake rufa mata baya a ziyara zuwa Washington ɗin, za su gana tare da shugaba Barack Obama da kuma wasu manyan jami'an gwamnatin Amirka, inda za su tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi halin da ake ciki a ƙasashen Larabawa da kuma rikicin da takardar kuɗin Euro ya faɗa ciki, kana da batun manufar da ta shafi makamashi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu