Ziyarar Jonathan a Borno da Yobe na shan suka
March 6, 2013Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban na Tarayyar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan zai ziyarci wadannan yankunan tun lokacin da hare-hare suka kazanta sama da shekara uku da suka shude. Al'ummar wannan yaki na ganin cewa shugaban da ma daukacin mukarraban ba na nuna halin ko oho wata kila don jam'iyyun adawa ne mulki a jihohin na Borno da Yobe. Tun a makon da ya wuce ne gwamnonin adawa suka zaga garin har ma shiga kasuwa duk da barazanar da ake musu na gamuwa da tashin Bama-Bamai. Haka kuma gwamnonin adawan sun ba da gudumowar Naira Miliyan 200 ga jihohin da abin ya shafa.
Matsayin kungiyoyi game da ziyarar Jonthan
Kungiyoyin da ke kare muradun arewacin Najeriya sun shafe kwanki biyu suna nazari a birnin kaduna tare da fitar da matsayinsu game da wannan ziyara ta Jonthan a borno da Yobe. Jagoran wanan gamayyar da ake yi wa lakabi da Citizens Arewa for Change, Ashir Sheriff ya danganta ziyarar da "yaudara daga Jonathan saboda shekaru hudu aka shafe ana cin zarafin mutane, ana kwace dukiyoyinsu ba tare da ya nuna tausayawa ga mutanen Maiduguri da kuma Damaturu ba."
Illolin hare hare a Arewacin Najeriya
Wasu mazauna yankin Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya sun nunar da cewa shugaban kasa ya yi fargar daji saboda ziyarar ta sa ba za ta amfani komai ba. Mutane da dama ne suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu sakamkon hare hare da aka kai a wadannan jihohi guda biyu. kana kungoyin taimakon raya kasa sun fice daga yankin na arewa i zuwa kudancin kasar. A daya hannun kuwa tattalin arzikin yankin ya durkushe. Saboda haka ne Ashir Sherif ya yi "Kira ga 'yan Borno da mutanen Yobe da ka da su fito su yi wa Jonthan maraba. Jami'an gwamnati ne ya kamata sun tare shi domin su baiyana ma sa irin laifin da ya yi wa mutanen Maiduguri."
Dukkanin jihohin da shugaban zai ziyar ta dai sun tsaurara matakan tsaro inda tuni aka rufe wasu hanyoyi da shugaban zai bi don tabbatar da cewa ya yi ziyayar ba tare da samun wani kalubale ba.
Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Mouhamadou Awal